Allahu Akbar: Labarin Wata Mata Da Kishiyarta

tw
Akwai wata mata itada kishiyarta, wacce take
mugun Qinta.
Wata Rana Mijinsu baya nan yayi tafiya,
sai Uwar
Gidan tayanke shawarar cewa: Idan dare
yayi zataje
ta kashe kishiyar ta domin ta huta da
ganinta.
Haka
kuwa akayi dare yanayi sai taje ta dauko
sabuwar wuka ta nufi Dakin Kishiyartata cikin
Fushi.
☼☼☼ALLAHU AKBAR☼☼☼
Kunsan kometagani kuwa??
Tana zuwa sai taga wannan matar a
kwance babu kai a jikinta, sai gangar jikin kawai
tagani, Razana da tsoro yakamata ta
takoma
dakinta
cikin Fargaba Har Gari ya waye bata
rintsaba. Da safiya tayi sai taje wajen kishiyar,
Abin mamaki
koda taje saita tararda matar a kicin tana
hada
Break Fast, Tace da ita Wance dan Allah
jiya Meya
faru dake da dare Sai Matar tace nadade
banji
dadin
Barci irin jiya ba, Sai kishiyar tayi
mamaki matuka tace to wacce Addu'a kika karanta da
zaki kwanta
bacci??
Sai ita wannan matar tace: Na karanta
wadannan
Surorin kafin na kwanta bacci kamar haka:

♣1. QULHUWALLAHU AHAD kafa Uku.
♣2. QUL A'UZU BIRABIL FALAQ kafa Uku.
♣3. QUL A'UZU BIRABIN NASS kafa Uku.
Na shafe iya kaina da ita, amma
tabbas na manta ban shafe jikina duka ba, Sai
tace:
Amma meyasa kikayi mini wannan
tambayar??
Sai Kishiyar ta sanar da ita duk abinda
yafaru. Kai in
takaice muku wannan shine sanadin
sulhunsu.
Yaku 'yan uwana mudaina raina
addu'a komai sanin da mukayi mata.
Domin wadansu da dama sun watsar da
wadannan
addu'oin kafin kwanciya bacci. Shiyasa
zakaji
mutum wani lokacin yana cewa: Ai jiya
nayi mugun
mafarki. Shiyasa nayi Tinanin nasake
tunatar
damu.
Allah ka rabamu da sharrin shedan
Allahu Akbar: Labarin Wata Mata Da Kishiyarta Allahu Akbar: Labarin Wata Mata Da Kishiyarta Reviewed by Unknown on December 16, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.