duniya da ke aikin hajji a Saudiya ke
tsayuwar Arfah a yau Alhamis, wanda shi ne
rukuni mai girma cikin rukunan aikin hajji.
Mahajjata na soma tsayuwar ne daga
fitowar alfijir zuwa faduwar rana, kuma
suna gudanar da ayyuka na Ibadah da suka
hada da yin addu’oi a filin na Arafah.
A Tsayuwar Arfa ba ana nufin mutum ya
tsaya ba hutawa tun safe har faduwar rana
ba, ana so ne mutum ya kasance a cikin filin
Arfah har zuwa faduwar rana.
Bayan hawan Arfa ne washegari al’ummar
musulmi a fadin duniya ke gudanar da
bukukuwan Sallar layya da aka fi sani da
sallah Babba a kasar Hausa.
Taron aikin Hajji shi ne taron mutane mafi
girma a duniya duk shekara.
Aikin Hajji yana cikin Shika-shikan
Musulunci guda biyar da aka wajabta wa
Musulmi ya gudanar akalla sau daya a
rayuwar shi idan har yana da wadata
kuma yana cikin koshin lafiya.
Alhazzai miliyan 2 na tsayuwar Arfah
Reviewed by Unknown
on
August 31, 2017
Rating:
No comments: