Nijeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar
zunzurutun kudi Dala Miliyan 21 (wanda ya
kai Naira biliyan 7.6) daga kudaden da ake
zargin tsohuwar ministar mai na kasar
Diezani Alison-Madueke ta sace a lokacin
tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta
kasar.
A jiya Litinin ne alkalin kotun mai shari'a
Abdulaziz Anka ya yanke wannan hukumcin
na kwace wadannan kudade da suke cikin
asusun ajiyanta a wani banki da kuma mika
shi ga gwamnatin Tarayyar Nijeriya.
Hukumar yaki da masu ta'annuti ga tattalin
arzikin Nijeriya din EFCC ce ta shigar da kara
kotun bayan da ta gano wadannan kudade
a wani banki da aka ajiye su a asusu
daban-daban don haka ta bukaci kotun da
ta mallaka wa gwamnatin kudaden don
kuwa a cewarta tana zargin tsohuwar
ministar ta same su ne ta hanyar da bata
dace ba.
Wannan dai ba shi karon farko da kotuna a
Nijeriya suke mallaka wa gwamnatin
kudaden da ake zargin tsohuwar ministan
ta sace ba. Ko a farkon watan nan ma dai
wata kotun ta mallaka wa gwamnatin
Nijeriya masu $40, (kimanin naira biliyan
14) da ake zargin tsohuwar ministan,
wacce ta ke fuskantar shari'a a Nijeriya da
kasar Birtaniyya, ta sace.
A wata sabuwa kuma wasu gungun
al'ummar Nijeriya sun gudanar da wani
jerin gwano a ofishin EFCC din da ke Abuja,
babban birnin Tarayyar Nijeriya suna masu
bukatar gwamnatin Birtaniyya da ta mika
Mrs Diezani ga mahukuntan Nijeriya don a
hukunta kan wadannan zargin da ake mata
na sace kudaden gwamnati.
Kotu Ta Sake Mallaka Wa Gwamnatin Nijeriya $21m Na Kudin Da Ake Zargin Diezani Ta Sace
Reviewed by Unknown
on
August 29, 2017
Rating:
No comments: