Sama da mutum dubu guda aka
tseratar
daga yankunansu bayan
mahaukaciyar
guguwar nan da ta afkawa jihar
Texax a
Amurka ta haifar da kakkarfan
ruwan
saman daya juye zuwa ambaliyar
ruwa a
Houston.
A cewar hukumar kula da yanayi
ta kasar,
karfi da kuma yawan ambaliyar
ruwan kan
ma’aunin centi mita 50 ba
kakkautawa ya
dakatar da zirga-zirga tare da
sanya razani
a zukatan mutanen yanki, lamarin
daya
tilasta kwashesu don kare
lafiyarsu.
Haka kuma yawan ruwan saman
ya sanya
koguna da dama yin ambaliya a
yankin abin
daya kara tsananta halin da
al’ummar ke
ciki, inda kuma masu aikin ceto
suka gaza
karasawa wasu wuraren da
annobar ta
tsananta.
Ya zuwa yanzu dai hukumomi sun
tabbatar
da mutuwar mutum biyu ciki har
da wata
mata da ruwa ya janyo gangar
jikinta kan
titi.
Tuni dai hukumomi suka yi gargadin
kauracewa zirga-zirga face wadanda suke a
yankunan da basa cikin hadarin samun
ambaliyar ko kuma wadanda aka kwashe
zuwa wasu yankunan.
Wannan dai ita ce mafi munin guguwa a
Amurka tun bayan ta Charley a watan
Agustan shekarar 2004 da kuma ta
Hurricane data afkawa Texas a shekarar
1961 wadda ta halaka mutum 34.
Mummunar guguwar ta haddasa
katsewar wutar lantarki a mafi yawancin
sassan jihar ta Texas, kuma yanzu haka
kimanin jami’an agaji dubu daya da dari
takwas ne ke aikin bayar da ceto
Mummunar guguwa ta juye Ambaliyar ruwa a Texas
Reviewed by Unknown
on
August 27, 2017
Rating:
No comments: