Buhari ya gana da shugabannin PDP


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun yi ganawar sirri da jagororin jam’iyyun APC da PDP a fadar gwamnatin kasar da ke birnin tarayya Abuja. Kamfanin Dillancin Labaran kasar, NAN ya rawaito cewa, ganawar wadda a aka fara ta tun da misalin karfe 11 na safe agogon kasar, Ahmed Makarfi shugaban jam'iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam'iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar. Ana ganin shugabannin na tattaunawa ne kan batutuwan da suka shafi siyasa da zamantakewar al’umma da kuma matsalar furta kalaman nuna kyamatar juna kamar yadda NAN ta yi Karin bayani. Wannan shi ne kusan karon farko da ake gudanar da irin wannan ganawar tun soma mulkin shugaban sama da shekaru biyu.
Buhari ya gana da shugabannin PDP Buhari ya gana da shugabannin PDP Reviewed by Unknown on August 25, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.