An fara gina Masallaci mafi girma kayatarwa a duniya a Swizalan


mafi kyau da kayatarwa a duniya a kasar Swizalan wadda na daya daga cikin kasashen Turai da Musulmai suke da yawa. Labaran da jaridar Duniya ta fitar na cewa, Kungiyar masallatan Juma'a ta Fribourg (Fribourg Mosques Association) ce ta ware kudi har dala miliyan 8 don gina Masallacin. Jaridar ta ci gaba da cewa, a hawa na farko na Masallacin za a dinga yin ibada. Sauran bangarorin Masallacin kuma za a bar su don yi wasu abubuwa na daban. Akwai wuraren motsa jiki na maza da mata a Masallacin, wurin wanka da wasan ninkaya ma na daga cikin abubuwan da za a samar. Akwai kuma gidaje da za a bayar haya a hawa na 4 da na 5 na Masallacin. An kuma ware wa yara kanana dakunan koyon amfani da na'urar kwamfuta. Akwai kuma dakunan karatu na musamman.
An fara gina Masallaci mafi girma kayatarwa a duniya a Swizalan An fara gina Masallaci mafi girma kayatarwa a duniya a Swizalan Reviewed by Unknown on August 25, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.