Results for Labarai

Ko kun san yadda Atiku ya shiga Amurka

February 05, 2019


Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu damar ziyartar Amurka ne makwanni biyu da suka shude bayan mahukuntan kasar sun dage masa haramcin ba shi Bisa na wucen-gadi kamar yadda Kamfanin Dillanci Labarai na Reuters ya rawaito.Amurka ta soke bai wa Atiku Bisa ne saboda zargin sa da aikata laifin cin hanci da rashawa, yayin da majiyoyi ke cewa, an ba shi damar shiga kasar ne bayan wasu ‘yan siyasa sun nema masa alfarma daga wurin ‘yan Majalisar Dokokin Kasar. ‘Yan neman alfarmar sun fake da cewa, bai kamata gwamnatin Amurka ta yi watsi da babban dan takarar da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari ba a zaben watan Fabairu na 2019. Wata majiya ta shaida wa Reuters cewa, Amurka ta bude wa Atiku kofa ne saboda gudun tabarbarewar alaka da shi da zaran ya samu nasara a zaben shugabancin Najeriya wadda ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika. Rotanni na cewa, Atiku ne ya dauki nauyin ‘yan siyasar da suka nema masa alfarma a wurin ‘Yan Majalisar Amurka har suka shawo kan Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar game da ziyarar tasa. Batun hana Atiku Bisa ya samo asali ne bayan zargin sa da karbar na goro daga wani wakilin Amurka, William Jefferson da zummar fadada harkar fasaha a Najeriya. Tun a shekarar a shekarar 2009 aka tuhumi Jefferson a Amurka tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari. Koda yake daga bisani an rage masa tsawon shekarun zama gidan yarin. Kazalika Amurka ta zargi cewa, daya daga cikin matan Atiku hudu, ta taimaka masa wajen tura sama da Dala miliyan 40 zuwa Amurka, (kudaden da aka diga ayar tambaya akan su) kuma ana zargin cewa, akalla Dala 1.7 daga cikinsu, ya karba ne a matsayin cin hanci daga wani kamfanin Siemens na Jamus.
Ko kun san yadda Atiku ya shiga Amurka Ko kun san yadda Atiku ya shiga Amurka Reviewed by Unknown on February 05, 2019 Rating: 5

Wata Mata Ta Gina Gida Da Sana'ar kafinta (Binta Muhd)

December 22, 2017
tw
Malama Binta Muhamamd wacce aka fi sani da Binta Maicarbi kafinta ce da ke gudanar da sana’ar kafinta a unguwar Kabuga cikin Jihar Kano. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa ta fara sana’arta ne da Naira dubu daya wacce a yanzu ta kai ga gina gidan kanta da ribar da take samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me ya ja ra’ayinki kika shiga sana’ar kafinta duba da cewa ana ganin sana’a ce
Na maza?

Zan iya cewa sha’awa ce kawai da kuma rabo. Da na fara kuma sai na ji ina son abin don haka na kara jajircewa don na nuna wa duniya cewa mata ma jarumai ne wajen neman na kansu. Duk da cewa ba komai ne mace za ta iya yi ba, amma akwai abubuwa da dama da mata za mu yi kamar maza. Ga shi yanzu na dauki kimanin shekara 17 ina wannan sana’a. Ina yin aikin gado da kujeru da sauransu. Babu abin da ba na yi na aikin sarrafa katako tun daga kan fila da feshi da sanya yadin kujeru. Nakan je titin France rod na sayo katakona da sauran kayan aikin sai na zo na yi aikin goge shi. Daga nan sai na yanka na fitar da kowane abu da nake son kerawa sawa’un gado ne ko kuma kujeru. Idan na gama sai na zo na sa pila in goge. Sannan idan suka bushe sai in kunna inji na goge su wato na yi musu feshin fenti. Duk da cewa mun fi yin sababbin kaya, amma muna sayen tsofaffin kaya don sayarwa kodayake a lokuta da dama sai na sake gyara su sannan nake sayar da su. Shin kin fuskanci kyama daga wurin ‘yan uwanki mata ko kuma abokan sana’arki maza wadanda za su ga sana’arsu ce kika yi wa shisshigi? A gaskiya da farko na fuskanci wannan matsala, amma a yanzu da rayuwa ta sauya kowa ya fito neman na kansa mun zama abin sha’awa a tsakanin ‘yan uwana mata, domin a yanzu da kansu suke zuwa sayen kayana, kuma su kawo min masu saye har ma na ba su wani abu. Haka kuma su kansu maza kafintocin sun nuna min kyama domin za ki ga yadda suke kushe wa mutum aiki a maimakon su karfafe shi. A wasu lokuta ma zan so shago na tarar an kone min kaya, amma da na yi hakuri ga shi komai ya wuce. A matsayinki na mace yaya kike yi wajen hada aikin gida da kuma sana”arki? A baya dai na sha wahala ta zirga-zirga, amma cikin ikon Allah da yake na kuduri aniyar cewa zan iya yi sannan kuma maigidana ya bani goyon baya, hakan na rika hada wadanan abubuwa biyu. Cikin ikon Allah ga shi har yanzu muna ci gaba da yi. Yanzu kuwa abin ya yi sauki domin ina da budurwar yarinya a gida wacce take taimaka min da ayyukan gida. Yawanci ina zuwa shago da misalin karfe 11 na safe sannan aduk lokacin da karfe hudu ta yi to na koma gida. Sai dai idan da wani abu muhimmi da zai tsayar da ni. Wacce nasara kike jin kin samu daga wannan sana’a? Babu shakka ina takama da wannan sana’a tawa, domin da ita nake rike da iyayena da ‘yan uwana. Baya ga filaye da na mallaka da wannan sana’a na gina gida. Haka kuma na mallaki shaguna da nake zuba kayana a ciki. Alhamdulillahi babu abin da zan ce sai godiya. Idan an duba na fara wannan sana’a ne da Naira dubu daya kacal. A wancan lokaci nakan je na sayi ‘yan kayan katako na hannu na kai wa masu saye su saya. Yau da gobe ina yin haka har na sami jari na fara wannan sana’a. Wane irin matsaloli kike fuskanta a wannan sana’ar? A gaskiya akwai kalubale musamman wasu lokutan mutane za su sanya a yi musu aiki a dauka akai musu wasu garuruwa kamar Zariya da Zamfara da Fatuskum, bayan mutum ya sa kudinsa ya yi aikin ga kuma kudin motar daukar kaya da ya biya, idan aka kai musu kayan sai su ki biyan kudin. A wasu lokutan kuma mutane suna sanya wa a yi musu aiki sai kuma su kasa biyan cikon kudin kayan, haka za a bar mutum da kaya sai dai ya saka a kasuwa. Mmutane nawa ne ke karkashinki? Kin san da yake mutanen suna zuwa suna tafiya ne. idan mutum ya dade a hannuna ya koyi aiki nakan yaye shi shi ma ya je ya kafa nasa shagon don cin gashin kansa. A yanzu haka irin wadanan mutane suna nan suna gudanar da sana’arsu ta kafinta a wurare daban-daban. A halin yanzu dai akwai mutane takwas da ke zuwa su yi aiki a karkashina wadanda kuma suke samin na abinci a kullum. A lokuta da dama ana kuka da ku kafintoci game da rashin cika alkawari me za k ice akan hakan? Gaskiya ne wannan, wanda kuma a tunanina hadama ce take kawo hakan. Ban sani ba ko don kasancewata mace ba na hada wa kaina aiki da yawa, ma’ana idan na ga aiki ya yi min yawa idan an kawo min aiki nakan gaya wa mutam halin da ake ciki, inda nake kai su wasu wuraren. Wace shawara za ki ba ‘yan uwanki kafintoci a kan hakan? Ina shawartarsu da su rike gaskiya da amana, domin duk abin da mutum zai yi idan babu wadannan abubuwa to ba zai sami nasara ba. A mastayinka na kafinta idan har mutum ya nemi ka yi masa aiki har ya dauki kudinsa ya ba ka kuka tsayar da lokaci to kamata ya yi ka yi kokari ka yi masa. A gaskiya Allah Ya yi wa wannan sana’a tamu albarka, akwai rufin asiri a cikinta. Wane kira kike da shi ga gwamnati ta yadda za a inganta muku wannan sana’a taku? Ina ganin ya kamata gwamnati ta dube mu musamamn matan da ke cikin wannan sana’a ta yi kokarin bunkasa mana wannan sana’a tamu ta hanyar ba mu jari sosai yadda za mu rika gudanar da wannan sana’a. A wasu lokutan kin san yadd mata suke babu karfin jari, sai ki ga abubuwan ba sa yin daidai. Muna bukatar gwamnati ta kawo mana dauki. Muna bukatar kayan aiki na zamani saboda har yanzu da tsofaffin kayayyaki muke amfani. Muna so kuma gwamnati ta ba mu fili da za mu rika zuba kayanmu idan mun kera. Zan kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan uwana mata da mu tashi mu nemi na kanmu kasancewar zamnani ya canza dole sai mace tana neman na kanta sanann abubuwan gida suke tafiya daidai. Ba duk namiji ne zai iya biya wa mace bukatunta ba. Ina kishin na ga ‘ya mace tana kwance babu sana’a. don haka akwai bukatar mata su tashi su jajirce domin su dogara da kansu.
Menene Ra'ayin Ku Gameda Binta Karfinta
Wata Mata Ta Gina Gida Da Sana'ar kafinta (Binta Muhd) Wata Mata Ta Gina Gida Da Sana'ar kafinta (Binta Muhd) Reviewed by Unknown on December 22, 2017 Rating: 5

Karin Bayani Game da Yadda Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi

November 20, 2017
tw
Maryam & Bilyamin
tw
Maryam & Bilyamin

Wani abokin marigayi Bilyamin Muhammed Bello, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa Maryam Sanda a daren Asabar 18 ga watan Nuwamba, Habib Gajam ya bayyana yadda lamarin ya auku.
Jaridar Inside Arewa ta ruwaito Gajam
yana fadin cewa bai taba ganin tashin
hankali a rayuwarsa ba tare da rashin
kunya irin wanda ya gani a kisan
Bilyaminu. Gajam yace rikicin ya samo asali ne da
misalin karfe 9 zuwa 10 na daren
Asabar, a gidan ma’auratan, inda
Maryam ta bukaci Bilyamin ya sake ta,
idan ba haka kuma zata yanke masa
mazakuta, wanda hakan ya sa abokinsa Ibrahim Aliero shiga tsakaninsu har sau
hudu, a lokacin da Maryam tayi yunkurin
caka masa wuka.
Ganin yadda lamarin ke neman yin
kamari, majiyar NAIJ.com ta ruwaito Gajam yana bayyana cewa hakan yasa
Ibrahim Aliero kiran wani kawun
Maryam, mai suna Auta, sa’annan ya kira
wani dan uwan Bilyamin, mai suna Abba,
don su zo su shiga tsakanin ma’auratan.
Ana cikin zaman jiransu, sai Maryam ta
fasa kwalban gyada, ta taso ma Bilyamin
zata kashe shi da kwalbar, amma sai
Bilyamin ya rike hannuwanta, har ya ji
ciwo a hannusa, sa’annan kuma ta cije
shi a yantsan hannu. Ba da dadewa ba sai Kawunta Auta ya
iso gidan, inda ya ja hankalinsu, tare da
yi musu nasiha, nan take dukkaninsu
suka amince masa da zasu zauna lafiya,
daga nan yayi tafiyarsa, inda shima
Ibrahim ya raka Bilyamin zuwa wani shagon magani, aka duba masa
hannunsa da Maryam ta cije shi, sa’annan
suka garzaya ATM ya cira kudi, don biyan
kudin gyaran motar Matar tasa. Sai da misalin karfe 11 na dare suka
koma gida, inda Ibrahim ya cigaba da
zama da ma’auratan har zuwa karfe 12
na dare, yana basu hakuri tare da tausan
su, daga nan ya tashi ya nufi gida.
Kwatsam da misalin karfe 2 na ranar
Lahadi, sai aka gayyace su zuwa asibitin
Maitama, inda Bilya ke kwance rai
kwafai mutu kwafai, jini ta ko ina, ga
saran wuka a kirjinsa, kafada, cinya, da
shaidan hakori a cikinsa. Gajam yace Maryam ta amsa laifinta a
Asibiti, amma da aka je Caji Ofis sai
labari ya sha bam bam, inda yace Maryam
tace ita ba ita ta kashe Bilyamin ba, a
sanadiyyar fadar da suka yi ne ya yanke
da tukunyar shisha, wanda hakan ne yayi sanadiyyan mutuwarsa. Da aka je gidan su, inda lamarin ya auku,
kamar yadda kwamishinan Yansanda ya
umarta, sai aka tarar da dakin a share
Tsaf Tsaf, ta wanke jinin daya zuba, ta yar
da makamin da tayi amfani dasu,
sa’annan ta fasa tukunyar shishan da tukunyar plawan dake dakin. A yanzu dai ana cigaba da gudanar da
bincike don tabbatar da gaskiyar
lamarin.
Karin Bayani Game da Yadda Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi Karin Bayani Game da Yadda  Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon  Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi Reviewed by Unknown on November 20, 2017 Rating: 5

Kotu Ta Sake Mallaka Wa Gwamnatin Nijeriya $21m Na Kudin Da Ake Zargin Diezani Ta Sace

August 29, 2017
tw Wata kotun tarayya da ke birnin Legas a
Nijeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar
zunzurutun kudi Dala Miliyan 21 (wanda ya
kai Naira biliyan 7.6) daga kudaden da ake
zargin tsohuwar ministar mai na kasar
Diezani Alison-Madueke ta sace a lokacin
tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta
kasar.
A jiya Litinin ne alkalin kotun mai shari'a
Abdulaziz Anka ya yanke wannan hukumcin
na kwace wadannan kudade da suke cikin
asusun ajiyanta a wani banki da kuma mika
shi ga gwamnatin Tarayyar Nijeriya.
Hukumar yaki da masu ta'annuti ga tattalin
arzikin Nijeriya din EFCC ce ta shigar da kara
kotun bayan da ta gano wadannan kudade
a wani banki da aka ajiye su a asusu
daban-daban don haka ta bukaci kotun da
ta mallaka wa gwamnatin kudaden don
kuwa a cewarta tana zargin tsohuwar
ministar ta same su ne ta hanyar da bata
dace ba.
Wannan dai ba shi karon farko da kotuna a
Nijeriya suke mallaka wa gwamnatin
kudaden da ake zargin tsohuwar ministan
ta sace ba. Ko a farkon watan nan ma dai
wata kotun ta mallaka wa gwamnatin
Nijeriya masu $40, (kimanin naira biliyan
14) da ake zargin tsohuwar ministan,
wacce ta ke fuskantar shari'a a Nijeriya da
kasar Birtaniyya, ta sace.
A wata sabuwa kuma wasu gungun
al'ummar Nijeriya sun gudanar da wani
jerin gwano a ofishin EFCC din da ke Abuja,
babban birnin Tarayyar Nijeriya suna masu
bukatar gwamnatin Birtaniyya da ta mika
Mrs Diezani ga mahukuntan Nijeriya don a
hukunta kan wadannan zargin da ake mata
na sace kudaden gwamnati.
Kotu Ta Sake Mallaka Wa Gwamnatin Nijeriya $21m Na Kudin Da Ake Zargin Diezani Ta Sace Kotu Ta Sake Mallaka Wa Gwamnatin Nijeriya $21m Na Kudin Da Ake Zargin Diezani Ta Sace Reviewed by Unknown on August 29, 2017 Rating: 5

Mummunar guguwa ta juye Ambaliyar ruwa a Texas

August 27, 2017
tw


Sama da mutum dubu guda aka

tseratar

daga yankunansu bayan

mahaukaciyar

guguwar nan da ta afkawa jihar

Texax a

Amurka ta haifar da kakkarfan

ruwan

saman daya juye zuwa ambaliyar


ruwa a

Houston.

A cewar hukumar kula da yanayi

ta kasar,

karfi da kuma yawan ambaliyar

ruwan kan

ma’aunin centi mita 50 ba

kakkautawa ya

dakatar da zirga-zirga tare da

sanya razani

a zukatan mutanen yanki, lamarin

daya

tilasta kwashesu don kare

lafiyarsu.

Haka kuma yawan ruwan saman

ya sanya

koguna da dama yin ambaliya a

yankin abin

daya kara tsananta halin da

al’ummar ke

ciki, inda kuma masu aikin ceto

suka gaza

karasawa wasu wuraren da

annobar ta

tsananta.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi sun

tabbatar

da mutuwar mutum biyu ciki har

da wata

mata da ruwa ya janyo gangar

jikinta kan

titi.



Tuni dai hukumomi suka yi gargadin


kauracewa zirga-zirga face wadanda suke a

yankunan da basa cikin hadarin samun

ambaliyar ko kuma wadanda aka kwashe

zuwa wasu yankunan.
Wannan dai ita ce mafi munin guguwa a

Amurka tun bayan ta Charley a watan

Agustan shekarar 2004 da kuma ta

Hurricane data afkawa Texas a shekarar

1961 wadda ta halaka mutum 34.
Mummunar guguwar ta haddasa

katsewar wutar lantarki a mafi yawancin

sassan jihar ta Texas, kuma yanzu haka

kimanin jami’an agaji dubu daya da dari

takwas ne ke aikin bayar da ceto
Mummunar guguwa ta juye Ambaliyar ruwa a Texas Mummunar guguwa ta juye Ambaliyar ruwa a Texas Reviewed by Unknown on August 27, 2017 Rating: 5

Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu

August 23, 2017
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya fara girmama su da nuna musu ladabi da biyayya tw
Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya fara girmama su da nuna musu ladabi da biyayya. Trump ya yi jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a garin Phoenix inda ya ce, watakila alakar Amurka da Koriya ta Arewa ta dawo daidai. Babban Kwamandan Sojin Amurka na Tekun Pacific Admiral Harry Harris kuma cewa, ya yi sun zabi hanyar diplomasiyya wajen warware rikicin Nukiliya da makamai masu l,nzami na Koriya ta Arewa. Kamfanin dillancin labaran na Kyodo kuma ya sanar da cewa, Harris ya yi wa 'yan jarida bayani a sansanin soji na Osan da ke kusa da Seul babban birnin Koriya ta Kudu. Ya ce, a yanzu sun zabi bin hanyar diplomasiyya don warware rikicinsu da Koriya ta Arewa. Ya kuma yi nuni da bukatar karfin soji ya taimaka wa aiyukan na diplomasiyya.
Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu Reviewed by Unknown on August 23, 2017 Rating: 5

'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya'

August 19, 2017
tw
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha
alwashin mayar da martani mai zafi ga duk
wata barazana da kasar Koriya ta Arewa
take yi wa kasarsa.
Ya ce martanin zai zama "wanda ba a taba
ganin irin shi ba a tarihin duniya".
A halin da ake ciki yanzu, Koriya ta Arewa na
yin barazanar kaddamar da harin makami
mai linzami a yankin tsibirin Guam da ke
Amurka, inda mutum 163,000 ke zaune.
Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton
cewa, Koriya ta Arewa na kokarin samun
nasara wajen rage rikicin makami mai
linzamin da zai iya shafar wasu kasashe,
wani abin da Amurka da kawayenta na
Asiya suka dade suna fargabar faruwarsa.
Ko wannan wata alama ce ta shiga filin daga
don kece rainin?
Masu sharhi sun ce kar ku tayar da hankali
kan wannan batu tukunna. Ga dalilan da
suka ba da:
1. Ba wanda yake son yaki
Wannan na daya daga cikin abubuwa masu
muhimmanci da ya kamata musa a ranmu.
Ba wanda yake son yakin don ba zai
taimakawa kowa ba.
Babban burin gwamnatin Koriya ta Arewa
shi ne samun kwanciyar hankali, kuma yaki
da Amurka ka iya jawo tsananin tashin
hankali.
Wakilin BBC kan al'amuran tsaro ya yi
bayanin cewa, duk wani harin Koriya ta
Arewa a kan Amurka ko kawayenta a yanzu
ka iya jawo gagarumin yakin da zai shafi
duniya, kuma ya dace mu sa a ranmu cewa
gwamntin Kim Jong-un ba ta kunar bakin-
wake ba ce.
A takaice, wannan ne ya sa Koriya ta Arewa
take iya kokarinta ta zama tana da karfin
makami mai linzami.
Samun wannan damar dalilai ne na yiyuwar
kare gwamnatin ta hanyar karin kudin
shiga.
Kim Jong-un ba ya so ya zama marigayi
Muammar Gaddafi na Libya, ko kuma
marigayi Saddam Hussein na Iraqi.
Andrei Lankov na Jami'ar Kookmin da ke
Seoul, ya shaida wa jaridar Guardian cewa,
"akwai yiyuwar samun tashin hankali",
amma Koriya ta Arewa ba ta da ra'ayin bin
hanyar diflomasiyya a wannan lokacin.
"Da farko suna son su samu damar cire
birnin Chicago daga taswirar duniya, sannan
kuma sai su nuna ra'ayinsu a kan mafita ta
bin hanyar diflomasiyya", in ji Mista Lnkov.
Amurka ta san cewa harin da za ta kai wa
Koriya ta Arewa zai tilasta wa Koriyar mayar
da martani kan kawayen Amurka, wato
kasashen Koriya ta Kudu da kuma Japan.
Wanda hakan zai jawo asarar rayuka da
suka hada da dubbban 'yan Amurka, da
sojoji da kuma fararen hula.
Dadin-dadawa, Washington ba ta bukatar
duk wata kasadar kaddamar da harin
makami mai linzamin da za a kai wa
Amurka.
2. Abin da kuke gani a baki ne kawai, amma
ba a filin daga ba
Shugaba Trump ya yi wa Koriya ta Arewa
barazana da kalamai marasa dadi, irin
kalaman da shugabannin Amurka ba su
saba furtawa ba, sai dai hakan ba ya nufin
Amurka a shirye take ta fara yakin ba.
Wani jami'in sojin Amurka da ya bukaci a
boye a sunansa ya shaida wa kamfanin
dillanci labarai na Reuters cewa, "saboda
kawai suna yin munanan kalamai, ba zai
sauya akidinmu ba".
Wani mai sharhi a jaridar New York Times,
Max Fisher, ya yi amannar cewa,"Wadannan
wasu kalamai ne na wasu mutane, amma ba
matsayin shugabanni ba, wanda shi ne jigo
a dangantaka tsakanin kasashe.".
Me ya yi saura, bayan gwajin makami mai
linzami guda biyu da Koriya Ta Arewa ta yi a
watan Yuli, Amurka ta dawo da dabarar
yadda za ta takura Koriya ta Arewa ta hanyar
takunkumin da Kwamitin Tsaro na Majalisar
Dinkin Duniya ta saka mata.
Kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawar
diflomasiyya mai ciki da kwarin gwiwa a
kan yiwuwar samun sulhu, inda suke samun
goyon baya daga China da kuma Rasha.
Wannan yana kalamai masu yin tafka da
warwara, amma kuma a bangare guda suna
sa Shugaba Trump yana shiga taitayinsa.
Duk da haka wasu masu sharhi na cewa,
rashin samun fahimtar juna kan iya jawo
yakin da ba a shirya masa ba.
3. Akwai lokacin da Amurka ta kusa gwabza
yaki da Koriya ta Arewa
Tsohon Mataimakin Sakataren Harkokin
wajen Amurka PJ Crowley ya yi bayanin
cewa, Amurka da Koriya ta Arewa sun fara
takaddama tun shekarar 1994, a lokacin da
Koriya ta Arewa ta ki amincewa ta bar wasu
maasu bincike na kasa da kasa su bincike
shirinta na kera makami mai linzami.
Daga nan ne harkokin diflomasiyya ya lalace.
A tsawon shekaru, Koriya ta Arewa ta sha
yin barazana ga Amurka, da Japan da kuma
Koriya ta Kudu, ta kuma sha yi wa
makwabciyarta barazana a lokuta daban-
daban.
Kalaman Trump na cike da abubuwa,
wadanda ba a taba jinsu ba daga wurin
wani shugaban Amurka ba.
Mista Crowley ya ce "Amurka ta sha fadar
cewa idan Koriya ta Arewa ta kuskura ta kai
mata hari, za ta kawo karshen gwamnatin
kasar."
Ya kara da cewa dan bambancin a nan shi
ne, shugaban Amurka ya ce zai iya fara kai
wa Koriyar hari, (kodayake daga bisani
Sakataren Harkokin Wajen kasar Rex
Tillerson ya kawar da yiwuwar hakan).
Masu sharhi sun ce, irin wadannan
abubuwa marasa dadi da ke fitowa daga
fadar White House ba a saba ganinsu ba,
wanda hakan ya sa ake damuwa.
Har yanzu Koriya ta Kudu wadda babbar
kawar Amurka ce, ita ce za ta fi fuskantar
matsala daga Koriya ta Arewa - wadda ita ko
damuwa ba ta yi.
4. Wanne tasiri yakin Amurka da Koriya zai yi
ga nahiyar Afirka?
Dokta Abubakar Kyari na Jami'ar Abuja ya ce
yakin ba zai yi wani tasiri ga kasashen Afirka
ba kai-tsaye saboda babu wata kasa a
nahiyar da take hulda da Koriya ta Arewa.
Ya ci gaba da cewa: "A baya Amurka ta yi
yake-yake da dama da wasu kasashe amma
hakan bai yi wani tasiri ga nahiyar ba."
Sai dai ya ce akwai fargabar cewa "Koriya ta
Arewa za ta iya kai wa sansanonin sojojin
Amurka da ke nahiyar Afirka," in ji shi.
Har ila yau, ya ce yakin zai iya shafar kasar
China - wadda take hulda sosai da kasashen
nahiyar "amma ba na ganin China za ta yi
fito na fito da Amurka."
Kyari ya ce babban abin tsoro game da yakin
shi ne yadda dukansu suke da makamin
kare dangi.
"Wannan babban al'amari ne saboda idan
aka yi maganar Nukiliya, ana maganar
makami ne da zai hallaka miliyoyin jama'a.
To ka ga wannan wani abu ne da zai iya
jawo Yakin Duniya na Uku, ko kuma tada
duniyar ma baki daya," a cewarsa.
Ya ce: "Yakin Amurka da Koriya ta Arewa ba
karamin bala'i ba ne don mutum ma ba zai
iya hasashen abin da zai faru ba."
'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya' 'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya' Reviewed by Unknown on August 19, 2017 Rating: 5

Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Kunan Bakin Waken Da Aka Kai Jihar Bornon Nigeriya

August 16, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren kunan bakin waken da aka kai garin Mandarari da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya a jiya Talata. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tofin Allah tsine tare da yin Allah wadai kan jerin hare-haren kunan bakin wake da wasu mata uku suka kai garin Mandarari da ke karamar Hukumar Konduga a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigetriya a yammacin jiya Talata, inda jerin hare-haren suka lashe rayukan mutane akalla 30 tare da jikkatan wasu fiye da 80 na daban. Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Mace ta farko ta tarwatsa kanta ce a tsakanin jama'a a cikin kasuwa, inda nan take mutane 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu mata biyu na daban suka tarwatsa kansu a kofar mashigar sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da kasuwar, inda suka jikkata mutane akalla 82. 'Yan kungiyar Boko Haram ne dai suka shahara da kai hare-haren kunan bakin wake a tsakanin jama'a a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.
Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Kunan Bakin Waken Da Aka Kai Jihar Bornon Nigeriya Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Kunan Bakin Waken Da Aka Kai Jihar Bornon Nigeriya Reviewed by Unknown on August 16, 2017 Rating: 5

Amurka: Muna son yin sulhu da Koriya ta Arewa, amma shawara ta rage gare ta

August 16, 2017

Ministan Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa, suna son su yi sulhu da Koriya ta Arewa amma fa shawara ta rage ga shugaban kasar Kim Jong-Un.Ministan Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa, suna son su yi sulhu da Koriya ta Arewa amma fa shawara ta rage ga shugaban kasar Kim Jong-Un. Tillerson ya tattauna da 'yan jaridu a yayin aton menama labarai da ya saba gudanarwa. Ya ce, har yanzu suna son yin sulhu da sasanta wa da Koriya ta Arewa. Ministan ya ki cewa komai game da kalaman da Amurkawa suke na cewa, Koriya ta Arewa na wasa da jelar wuta. A makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ko dai Koriya ta Arewa ta daina yi musu barazana ko kuma ta gane kurenta.
Amurka: Muna son yin sulhu da Koriya ta Arewa, amma shawara ta rage gare ta Amurka: Muna son yin sulhu da Koriya ta Arewa, amma shawara ta rage gare ta Reviewed by Unknown on August 16, 2017 Rating: 5

Aisha Buhari Za Ta Ziyarci Jahar Imo a Gobe Laraba

August 01, 2017
Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta kammala shiri tsaf na ziyartar jahar Imo a Gobe Laraba domin halartar taron watan Agusta da matan jahar ke yi a kowacce shekara.
Mai baiwa gwamnan jahar, Rochas Okorocha shawara akan harkokin mata, Dr Nnenna Ezebuiro ita ta bayyana haka a taron manema labarai a Owerri babban birnin jahar.
Ta ce banda uwargidan shugaba kasar wacce ita ce uwar taro, matan gwamnonin jahohi 35 su ma za su halarci taron.
Taron zai mayar da hankali ne akan hadin kan kasa, maimakon samar da abubuwan more rayuwa, saboda a cewar Ezebuiro, abunda kasar ke bukata kenan a yanzu haka.
Ta ce wannan ya sa suka gayyaci gaba daya matan gwamnoni kasar nan da matan shuwagabannin hukumonin tsaro.
Ta kara da cewa gwamna Okorocha zai yi amfani da damar wajen nunawa matan jahar Imo cewa suna da rawar da za su taka a ci gaban kasa.

Aisha Buhari Za Ta Ziyarci Jahar Imo a Gobe Laraba Aisha Buhari Za Ta Ziyarci Jahar Imo a Gobe Laraba Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Komawar Buratai Maiduguri za ta kawo karshen Boko Haram? kuwa

August 01, 2017
Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun isa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na yakar kungiyar Boko Haram.
A makon da ya gabata ne Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarce su da su koma can bayan wani mummunan hari da kungiyar ta kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 40.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya Janar Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa da sanyin safiyar ranar Talata ne hafsoshin son suka isa birnin, wanda shi ne cibiyar masu tayar da kayar bayan.
Ya ce babban Hafsan Hafsoshin kasar Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ne ya jagoranci sauran hafsoshin sojin da suka hada da shugaban sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai da na sama Air Marshal Sadique Abubakar.
Janar Kuka-Sheka ya ce babban hafsan rundunar sojin ruwa na kasar ne kawai ba ya cikin tawagar saboda ya yi tafiya, amma shi ma wakilansa na can.

Harin da Boko Haram ta kai wa tawagar masu binciken mai na NNPC, wanda shi ne mafi muni a bana da ta kai, ya tayar da hankalin al'ummar kasar.
Ya kuma janyo suka ga jami'an tsaron kasar, ganin yadda da farko suka ce sun kubutar da mutanen amma daga bisani sai Boko Haram ta fitar da hoton bidiyon wasu daga cikin mutanen.
Shugabannin sojin NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA baya ma an taba bai wa shugabannin sojin irin wannan umarni amma wasu na ganin bai yi tasiri ba
Sannan kuma rahotanni suka tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu ya karu matuka.
Tuni dai shugabannin sojojin suka isa babbar cibiyar gudanar da ayuukan soji da ke Maidugurin.
Ministan tsaron Najeriya ya ce za a sayi karin kayan aiki na zamani wadanda za su bai wa jami'an tsaro damar ganin abokan gaba daga nesa.
Mafi yawancin mutanen da aka kashe a harin na makon jiya a jihar Borno sojoji ne da 'yan sintiri ko kuma 'yan kato da gora.
Komawar Buratai Maiduguri za ta kawo karshen Boko Haram? kuwa Komawar Buratai Maiduguri za ta kawo karshen Boko Haram? kuwa Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33

August 01, 2017
Kungiyoyin kwadago suke zanga za
Bayanai daga jihar Kano na cewa kungiyar kwadagon jihar ta ce mambobinta na bin hukumomi makudan kudaden fansho da sauran hakkokin ma'aikata.
Kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya reshen jihar kano, ta ce ta na bin gwamnatin jihar kano bashin sama da Naira bilyan 33, a zaman kudin fansho da hakkin ma’aikata.
Saboda haka ne kungiyar kwadagon take tuni ga gwamnatin jihar da ta saka batun ma’aikata a sahun farko idan ta fara kasafta kudaden da ta samu daga hanun gwamnatin tarayya, wani kaso na biyan basussuka da jihohin na Najeriya suka karba, daga kasashen yammaci, sama da da abinda ya kamata su biya.
Wannan karon, jihar ta sami sama da Naira biliyan dubu 10.
Shugaban kungiyar kwadagon a jihar kano Comrade Kabiru Ado Minjibir ya ce ya koka kan yadda kusan ba’a la’akkari da wadanda suka jima suna dakon kudaden fanshon su.
Da yake magana kan wannan batu, kwamishinan kudi na jihar Farfessa Kabir Isa Dandago, ya yi alkawarin cewa jihar za ta mutunta sharuddan da gwamnatin tarayya ta shimfida game da yadda za su yi amfani da kudaden.
Wannan karo, gwamnatin tarayya ta na son su ware kashi 75% cikin dari na kudaden wajen biyan bukatun ma’aikata.
Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33 Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33 Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 23 a jihar Gombe

August 01, 2017
Wani mummunan labarin da muka samu na nuna cewa akalla mutane ashirin da uku ne suka gamu da ajalinsu a jihar Gombe bisa sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta rutsa da su. Haka ma dai ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar rushewar gidaje 12 bayan da aka shafe awowi da dama ana zabga mamakon ruwan kamar da bakin kwarya a garuruwan Dadin Kowa da Yemaltu-Deba duk dai a cikin jihar. 
Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 23 a jihar Gombe Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 23 a jihar Gombe Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci a bi mata hakkinta a Kaduna

August 01, 2017
Kungiyar 'yan Jaridu ta
Najeriya reshen Kaduna ta
bai wa rundunar 'yan sandar
jihar wa'adin makonni biyu ta
gudanar da sahihin bincike
tare da hukunta jami'inta.
Bukatar ya biyo bayan zargin da
ake wa jami’an da taimakawa
'yan bangar siyasa wajen tada
rikicin a lokacin taron manema
labarai da wasu jiga-jigan
jam'iyyar APC a jihar suka kira
domin nuna rashin gamsuwar
su da zaben wakilan jam'iyyar
zuwa babban taron ta na kasa.
Cikin wadanda suka halarci
taron sun hada da sanata
Suleman Hunkuyi da Sanata
Shehu Sani da kuma Isah Ashiru
kudan.
A saurare karin bayani a
Rahoton da wakilinmu na
Kaduna Aminu Sani Sado ya aiko
mana.
Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci
a bi mata hakkinta a Kaduna
Daga Umaymah Sani
Abdulmumi
Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci a bi mata hakkinta a Kaduna Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci a bi mata hakkinta a Kaduna Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Yan Neja Delta sun ba gwamnatin Najeriya wa’adi

August 01, 2017
Kungiyar Dattawan Yankin Neja
Delta a kudancin Najeriya ta ba
Gwamnatin kasar wa’adin
zuwa ranar 1 ga watan
Nuwamba ta biya bukatunta ko
kuma ta fice daga tattaunawar
samun zaman lafiya da suke yi
tsakaninsu.
Tawagar shugabannin a
karkashin Chief Edwin Clark ta
ce sun ba Gwamnati bukatun
16 cikinsu har da yaki da talauci
a Yankin domin kawo karshen
hare haren da ake kai kan
bututun mai, amma gwamnati
ta kasa aiwatarwa.
A watan Nuwamban bara ne
shugabannin yankin na Neja
Delta suka mikawa shugaba
Buhari bukatunsu 16, matakin
da ya takaita hare haren
tsagerun yankin akan kadarorin
gwamnati.
Bukatun sun hada da dawo da
dawo da manyan ofisoshin
kamfanonin mai zuwa kudancin
kasar da kara ware kudaden
tallafi domin ci gaban yankin.
Mista Clarke ya ce za su fice
tattaunawar idan har
gwamnati ta gaza cimma
bukatunsu.
Yan Neja Delta sun ba gwamnatin Najeriya wa’adi Yan Neja Delta sun ba gwamnatin Najeriya wa’adi Reviewed by Unknown on August 01, 2017 Rating: 5

Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Buhari Da Ya Janye Dokar Hana Shigo Da Shinkafa Da Mota

March 09, 2017
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ada Abubakar na 3 ya yi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta sassauta batundokar nan da ta hana shigo da shinkafa da motoci ta kan iyayokin kasa ta Nijeriya sai ta ruwa
Sarkin ya yi wannan kiran ne a jiya a lokacin da mukaddashin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Sokoto
Sarkin Musulmi ya ci gaba da bayyana cewa wadannan manufofi basu yi daidai da yanayin da kasar ke ciki ba a halin yanzu na tabarbarewar tattalin arziki
“Za mu ci gaba da zama muryar marasa murya (talaka), kuma a wannan nukuda, ba za mu gajiya da kiran gwamnati da ta yi dubu tare da sassauta wasu manufofi nata ba ta yadda talaka zai samu sa’ida” inji Sarkin Musulmi ya ce
“‘Yan Nijeriya na cikin mawuyacin hali, a saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta sassauta manufofinta ta yadda al’umma za ta samu sauki. Wannan ita ce hanyar da za ta samar da fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama’a”
“Muna jaddadawa gwamnati tabbacin hadin kanmu da goyon bayanmu a kowane lokaci, amma wadannan manufofi biyu sam sun zo a lokacin da bai dace ba.” A cewar Sarkin Musulmin Sa’ad Abubukar na 3
Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Buhari Da Ya Janye Dokar Hana Shigo Da Shinkafa Da Mota Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Buhari Da Ya Janye Dokar Hana Shigo Da Shinkafa Da Mota Reviewed by Unknown on March 09, 2017 Rating: 5
Older Posts Home
Powered by Blogger.