Karin Bayani Game da Yadda Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi

tw
Maryam & Bilyamin
tw
Maryam & Bilyamin

Wani abokin marigayi Bilyamin Muhammed Bello, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa Maryam Sanda a daren Asabar 18 ga watan Nuwamba, Habib Gajam ya bayyana yadda lamarin ya auku.
Jaridar Inside Arewa ta ruwaito Gajam
yana fadin cewa bai taba ganin tashin
hankali a rayuwarsa ba tare da rashin
kunya irin wanda ya gani a kisan
Bilyaminu. Gajam yace rikicin ya samo asali ne da
misalin karfe 9 zuwa 10 na daren
Asabar, a gidan ma’auratan, inda
Maryam ta bukaci Bilyamin ya sake ta,
idan ba haka kuma zata yanke masa
mazakuta, wanda hakan ya sa abokinsa Ibrahim Aliero shiga tsakaninsu har sau
hudu, a lokacin da Maryam tayi yunkurin
caka masa wuka.
Ganin yadda lamarin ke neman yin
kamari, majiyar NAIJ.com ta ruwaito Gajam yana bayyana cewa hakan yasa
Ibrahim Aliero kiran wani kawun
Maryam, mai suna Auta, sa’annan ya kira
wani dan uwan Bilyamin, mai suna Abba,
don su zo su shiga tsakanin ma’auratan.
Ana cikin zaman jiransu, sai Maryam ta
fasa kwalban gyada, ta taso ma Bilyamin
zata kashe shi da kwalbar, amma sai
Bilyamin ya rike hannuwanta, har ya ji
ciwo a hannusa, sa’annan kuma ta cije
shi a yantsan hannu. Ba da dadewa ba sai Kawunta Auta ya
iso gidan, inda ya ja hankalinsu, tare da
yi musu nasiha, nan take dukkaninsu
suka amince masa da zasu zauna lafiya,
daga nan yayi tafiyarsa, inda shima
Ibrahim ya raka Bilyamin zuwa wani shagon magani, aka duba masa
hannunsa da Maryam ta cije shi, sa’annan
suka garzaya ATM ya cira kudi, don biyan
kudin gyaran motar Matar tasa. Sai da misalin karfe 11 na dare suka
koma gida, inda Ibrahim ya cigaba da
zama da ma’auratan har zuwa karfe 12
na dare, yana basu hakuri tare da tausan
su, daga nan ya tashi ya nufi gida.
Kwatsam da misalin karfe 2 na ranar
Lahadi, sai aka gayyace su zuwa asibitin
Maitama, inda Bilya ke kwance rai
kwafai mutu kwafai, jini ta ko ina, ga
saran wuka a kirjinsa, kafada, cinya, da
shaidan hakori a cikinsa. Gajam yace Maryam ta amsa laifinta a
Asibiti, amma da aka je Caji Ofis sai
labari ya sha bam bam, inda yace Maryam
tace ita ba ita ta kashe Bilyamin ba, a
sanadiyyar fadar da suka yi ne ya yanke
da tukunyar shisha, wanda hakan ne yayi sanadiyyan mutuwarsa. Da aka je gidan su, inda lamarin ya auku,
kamar yadda kwamishinan Yansanda ya
umarta, sai aka tarar da dakin a share
Tsaf Tsaf, ta wanke jinin daya zuba, ta yar
da makamin da tayi amfani dasu,
sa’annan ta fasa tukunyar shishan da tukunyar plawan dake dakin. A yanzu dai ana cigaba da gudanar da
bincike don tabbatar da gaskiyar
lamarin.
Karin Bayani Game da Yadda Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi Karin Bayani Game da Yadda  Matar Bliyaminu, Yaron Tsohon  Minista, Bello Halliru Ta Kashe shi Reviewed by Unknown on November 20, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.