
(Ta Yaya Zan Dubo Suna Na? Sannan Yaya Sabo Zai Nema?)
↓
↓
↓
A Daren Jiya Ne Aka Saki Sunayen
Wadanda Suka Yi Nasara A Tsarin Nan Na
bada Tallafi Domin Magance Matsalar
Rashin Aikin Yi Na Gwamnatin Tarayya
Mai Lakabin N-POWER, Sai Dai Tun Daga
Jiyan Da Yawa Daga Al’ummar Mu Na Tayin Tambayoyi Dangane Da
Abinda Ya Shige Musu Duhu Akan
Wannan Batun, Hakan Yasa Nayi Wannan
Rubutu Domin Yin Bayani Akan Sa Domin
Dai Mu Gudu Tare Mu Kuma Tsira Tare,
<1.> Ga Sababbin Masu Neman Shiga
Cikin Shirin N-POWER Ina Basu
Shawara Da Suje [' Cafe '] Mafi Kusa
Da Su Domin Cike Musu Idan Kuma
Zasu Iya Yi Ta Wayoyin Su Na Zamani
Ma’ana Mutum Yana Da Kwarewa Akai To Zaije Shafin N-POWER Wato Npower.gov.ng
Shine Shafin Da Ake Yin Wannan Register
Idan Kaje Zaka Zabi Bangaren Da
Kake Son Cikewa,
<2.> Hanyoyin Da Ake Bi Wajen Duba
Sunayen Da Aka Saki Sune Kamar
Haka: KU ziyarci Npower.gov.ng/@n-power
Check Sai Ka Sanya Lambar Wayar Ka Ko E-mail Dinka Ko Kuma BVN Dinka A Akwatin Bincike (searching Box )
Idan Har Kayi Nasarar Shiga Zaka Ga
Cikakken Sunan Ka Ya Fito Daga Nan
Kuma Zasu Tura Maka Sako Ta wayarka
(Message) Sai Ka Shirya Tantancewa Wadda Ranar Da Za’a Ai Ta Zai Zo A
Kasa, Hanya ta biyu:
<1.> Ka Ziyarci
npower.gov.ng
Kayi “login”
<2.> Sai Ka Danna “check your pre-
selection status”.
< 3.> Sai Ka Sanya Lambar wayar ka, Ko
E-mail Dinka Ko Kuma BVN DinKa A
Akwatin bincike Wajen (searching Box)
Idan Har Kayi Nasarar Shiga ZakaGa
Cikakken Sunan Ka Ya Fito,
<4.> Daga Nan Kuma Zasu Tura Maka
Sako Ta wayarka (Message) Da Kuma Na
(E-mail) Na Tayawar Murnar Yin
Nasara A Zagaye Na Farko,
<5.> Daga Nan Saika Shirya Tantancewa
Ta Gaba Da Gaba Wanda Za’a
Gabatar Daga Ranar 27th November
Zuwa 8th, December Allah Yabada Sa.a
No comments: