Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta kammala shiri tsaf na ziyartar jahar Imo a Gobe Laraba domin halartar taron watan Agusta da matan jahar ke yi a kowacce shekara.
Mai baiwa gwamnan jahar, Rochas Okorocha shawara akan harkokin mata, Dr Nnenna Ezebuiro ita ta bayyana haka a taron manema labarai a Owerri babban birnin jahar.
Ta ce banda uwargidan shugaba kasar wacce ita ce uwar taro, matan gwamnonin jahohi 35 su ma za su halarci taron.
Taron zai mayar da hankali ne akan hadin kan kasa, maimakon samar da abubuwan more rayuwa, saboda a cewar Ezebuiro, abunda kasar ke bukata kenan a yanzu haka.
Ta ce wannan ya sa suka gayyaci gaba daya matan gwamnoni kasar nan da matan shuwagabannin hukumonin tsaro.
Ta kara da cewa gwamna Okorocha zai yi amfani da damar wajen nunawa matan jahar Imo cewa suna da rawar da za su taka a ci gaban kasa.

Aisha Buhari Za Ta Ziyarci Jahar Imo a Gobe Laraba
Reviewed by Unknown
on
August 01, 2017
Rating:

No comments: