Ministan Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa, suna son su yi sulhu da Koriya ta Arewa amma fa shawara ta rage ga shugaban kasar Kim Jong-Un.

Ministan Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa, suna son su yi sulhu da Koriya ta Arewa amma fa shawara ta rage ga shugaban kasar Kim Jong-Un.
Tillerson ya tattauna da 'yan jaridu a yayin aton menama labarai da ya saba gudanarwa.
Ya ce, har yanzu suna son yin sulhu da sasanta wa da Koriya ta Arewa.
Ministan ya ki cewa komai game da kalaman da Amurkawa suke na cewa, Koriya ta Arewa na wasa da jelar wuta.
A makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ko dai Koriya ta Arewa ta daina yi musu barazana ko kuma ta gane kurenta.
No comments: