Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren kunan bakin waken da aka kai garin Mandarari da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya a jiya Talata.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tofin Allah tsine tare da yin Allah wadai kan jerin hare-haren kunan bakin wake da wasu mata uku suka kai garin Mandarari da ke karamar Hukumar Konduga a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigetriya a yammacin jiya Talata, inda jerin hare-haren suka lashe rayukan mutane akalla 30 tare da jikkatan wasu fiye da 80 na daban.
Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Mace ta farko ta tarwatsa kanta ce a tsakanin jama'a a cikin kasuwa, inda nan take mutane 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu mata biyu na daban suka tarwatsa kansu a kofar mashigar sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da kasuwar, inda suka jikkata mutane akalla 82. 'Yan kungiyar Boko Haram ne dai suka shahara da kai hare-haren kunan bakin wake a tsakanin jama'a a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.
No comments: