'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya'

tw
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha
alwashin mayar da martani mai zafi ga duk
wata barazana da kasar Koriya ta Arewa
take yi wa kasarsa.
Ya ce martanin zai zama "wanda ba a taba
ganin irin shi ba a tarihin duniya".
A halin da ake ciki yanzu, Koriya ta Arewa na
yin barazanar kaddamar da harin makami
mai linzami a yankin tsibirin Guam da ke
Amurka, inda mutum 163,000 ke zaune.
Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton
cewa, Koriya ta Arewa na kokarin samun
nasara wajen rage rikicin makami mai
linzamin da zai iya shafar wasu kasashe,
wani abin da Amurka da kawayenta na
Asiya suka dade suna fargabar faruwarsa.
Ko wannan wata alama ce ta shiga filin daga
don kece rainin?
Masu sharhi sun ce kar ku tayar da hankali
kan wannan batu tukunna. Ga dalilan da
suka ba da:
1. Ba wanda yake son yaki
Wannan na daya daga cikin abubuwa masu
muhimmanci da ya kamata musa a ranmu.
Ba wanda yake son yakin don ba zai
taimakawa kowa ba.
Babban burin gwamnatin Koriya ta Arewa
shi ne samun kwanciyar hankali, kuma yaki
da Amurka ka iya jawo tsananin tashin
hankali.
Wakilin BBC kan al'amuran tsaro ya yi
bayanin cewa, duk wani harin Koriya ta
Arewa a kan Amurka ko kawayenta a yanzu
ka iya jawo gagarumin yakin da zai shafi
duniya, kuma ya dace mu sa a ranmu cewa
gwamntin Kim Jong-un ba ta kunar bakin-
wake ba ce.
A takaice, wannan ne ya sa Koriya ta Arewa
take iya kokarinta ta zama tana da karfin
makami mai linzami.
Samun wannan damar dalilai ne na yiyuwar
kare gwamnatin ta hanyar karin kudin
shiga.
Kim Jong-un ba ya so ya zama marigayi
Muammar Gaddafi na Libya, ko kuma
marigayi Saddam Hussein na Iraqi.
Andrei Lankov na Jami'ar Kookmin da ke
Seoul, ya shaida wa jaridar Guardian cewa,
"akwai yiyuwar samun tashin hankali",
amma Koriya ta Arewa ba ta da ra'ayin bin
hanyar diflomasiyya a wannan lokacin.
"Da farko suna son su samu damar cire
birnin Chicago daga taswirar duniya, sannan
kuma sai su nuna ra'ayinsu a kan mafita ta
bin hanyar diflomasiyya", in ji Mista Lnkov.
Amurka ta san cewa harin da za ta kai wa
Koriya ta Arewa zai tilasta wa Koriyar mayar
da martani kan kawayen Amurka, wato
kasashen Koriya ta Kudu da kuma Japan.
Wanda hakan zai jawo asarar rayuka da
suka hada da dubbban 'yan Amurka, da
sojoji da kuma fararen hula.
Dadin-dadawa, Washington ba ta bukatar
duk wata kasadar kaddamar da harin
makami mai linzamin da za a kai wa
Amurka.
2. Abin da kuke gani a baki ne kawai, amma
ba a filin daga ba
Shugaba Trump ya yi wa Koriya ta Arewa
barazana da kalamai marasa dadi, irin
kalaman da shugabannin Amurka ba su
saba furtawa ba, sai dai hakan ba ya nufin
Amurka a shirye take ta fara yakin ba.
Wani jami'in sojin Amurka da ya bukaci a
boye a sunansa ya shaida wa kamfanin
dillanci labarai na Reuters cewa, "saboda
kawai suna yin munanan kalamai, ba zai
sauya akidinmu ba".
Wani mai sharhi a jaridar New York Times,
Max Fisher, ya yi amannar cewa,"Wadannan
wasu kalamai ne na wasu mutane, amma ba
matsayin shugabanni ba, wanda shi ne jigo
a dangantaka tsakanin kasashe.".
Me ya yi saura, bayan gwajin makami mai
linzami guda biyu da Koriya Ta Arewa ta yi a
watan Yuli, Amurka ta dawo da dabarar
yadda za ta takura Koriya ta Arewa ta hanyar
takunkumin da Kwamitin Tsaro na Majalisar
Dinkin Duniya ta saka mata.
Kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawar
diflomasiyya mai ciki da kwarin gwiwa a
kan yiwuwar samun sulhu, inda suke samun
goyon baya daga China da kuma Rasha.
Wannan yana kalamai masu yin tafka da
warwara, amma kuma a bangare guda suna
sa Shugaba Trump yana shiga taitayinsa.
Duk da haka wasu masu sharhi na cewa,
rashin samun fahimtar juna kan iya jawo
yakin da ba a shirya masa ba.
3. Akwai lokacin da Amurka ta kusa gwabza
yaki da Koriya ta Arewa
Tsohon Mataimakin Sakataren Harkokin
wajen Amurka PJ Crowley ya yi bayanin
cewa, Amurka da Koriya ta Arewa sun fara
takaddama tun shekarar 1994, a lokacin da
Koriya ta Arewa ta ki amincewa ta bar wasu
maasu bincike na kasa da kasa su bincike
shirinta na kera makami mai linzami.
Daga nan ne harkokin diflomasiyya ya lalace.
A tsawon shekaru, Koriya ta Arewa ta sha
yin barazana ga Amurka, da Japan da kuma
Koriya ta Kudu, ta kuma sha yi wa
makwabciyarta barazana a lokuta daban-
daban.
Kalaman Trump na cike da abubuwa,
wadanda ba a taba jinsu ba daga wurin
wani shugaban Amurka ba.
Mista Crowley ya ce "Amurka ta sha fadar
cewa idan Koriya ta Arewa ta kuskura ta kai
mata hari, za ta kawo karshen gwamnatin
kasar."
Ya kara da cewa dan bambancin a nan shi
ne, shugaban Amurka ya ce zai iya fara kai
wa Koriyar hari, (kodayake daga bisani
Sakataren Harkokin Wajen kasar Rex
Tillerson ya kawar da yiwuwar hakan).
Masu sharhi sun ce, irin wadannan
abubuwa marasa dadi da ke fitowa daga
fadar White House ba a saba ganinsu ba,
wanda hakan ya sa ake damuwa.
Har yanzu Koriya ta Kudu wadda babbar
kawar Amurka ce, ita ce za ta fi fuskantar
matsala daga Koriya ta Arewa - wadda ita ko
damuwa ba ta yi.
4. Wanne tasiri yakin Amurka da Koriya zai yi
ga nahiyar Afirka?
Dokta Abubakar Kyari na Jami'ar Abuja ya ce
yakin ba zai yi wani tasiri ga kasashen Afirka
ba kai-tsaye saboda babu wata kasa a
nahiyar da take hulda da Koriya ta Arewa.
Ya ci gaba da cewa: "A baya Amurka ta yi
yake-yake da dama da wasu kasashe amma
hakan bai yi wani tasiri ga nahiyar ba."
Sai dai ya ce akwai fargabar cewa "Koriya ta
Arewa za ta iya kai wa sansanonin sojojin
Amurka da ke nahiyar Afirka," in ji shi.
Har ila yau, ya ce yakin zai iya shafar kasar
China - wadda take hulda sosai da kasashen
nahiyar "amma ba na ganin China za ta yi
fito na fito da Amurka."
Kyari ya ce babban abin tsoro game da yakin
shi ne yadda dukansu suke da makamin
kare dangi.
"Wannan babban al'amari ne saboda idan
aka yi maganar Nukiliya, ana maganar
makami ne da zai hallaka miliyoyin jama'a.
To ka ga wannan wani abu ne da zai iya
jawo Yakin Duniya na Uku, ko kuma tada
duniyar ma baki daya," a cewarsa.
Ya ce: "Yakin Amurka da Koriya ta Arewa ba
karamin bala'i ba ne don mutum ma ba zai
iya hasashen abin da zai faru ba."
'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya' 'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya' Reviewed by Unknown on August 19, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.