Fadar shugaban Nigeria ta ce nan gaba a
yau Assabar ne ake sa ran Shugaban kasar
Muhammadu Buhari zai koma kasar bayan
wata doguwar jinya a London.
A cikin wata sanarwa da Mai bai wa
shugaban Shawara kan watsa labarai Femi
Adesina ya fitar ya ce ana sa ran shugaban
ya yi wa 'yan kasar jawabi ta gidajen radiyo
da tallabijin ranar Litinin da safe.
''Ya gode wa daukacin 'yan Nigeria
wadanda suka yi ta yi masa addu'ar samun
lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara
kwantawa ciwo,'' inji takaitacciyar sanarwar
mai sakin layi hudu.
Shugaba Buhari dai ya bar kasar ne ranar 7
ga watan Mayu domin jinyar rashin lafiyar
da ba a bayyana ba; bayan ya mika
ragwamar shugabancin kasar ga
mataimakinsa wanda ya kasance
mukaddashin shugaban kasar tun sannan.
Wannan dai shi ne lokaci mafi tsawo da
wani shugaban kasar ya taba kwashewa
yana jinya a kasar waje kuma dawowar tasa
na zuwa ne 'yan kwanakki bayan da wasu
'yan kasar suka fara zanga-zanga suna kiran
ya dawo ko yayi murabus.
Subscribe to:
Post Comments
(
Atom
)
No comments: