Saudiyya ta ba wa Maniyyatan Qatar damar zuwa Aikin Hajjin bana

center
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da bayar
da dama ga Maniyyatan Qatar kan su
halari Aikin Hajjin bana kuma Sarkin
Saudiyya Salman dan Abdulaziz ne zai
dauki dawainiyarsu.
Kamfanin dillancin labaran na Saudiyya
SPA ya sanar da cewa, Sarkin na
Saudiyya ya karbi shawawarar dansa
kuma Yariman kasar Muhammad bin
Salman na cewa, Maniyyatan Qatar su yi
amfani da kofar kan iyaka ta Selwa.
An bayyana cewa, an amince da
wannan shawara ne bayan da daya
daga cikin iyalan Al-Thani na Qatar wato
Shaikh Abdullah bin Ali bin Abdullah bin
Casim Al-Thani ya gana da yariman
Muhammad a fadar Assalam da ke
Jeddah.
A yanzu haka dai Sarki Salman ya
amince da jama'ar Qatar su je aikin Hajji
ba tare da an tantance su a filayen tashi
da saukar jiragen sama ba.
Saudiyya ta ba wa Maniyyatan Qatar damar zuwa Aikin Hajjin bana Saudiyya ta ba wa Maniyyatan Qatar damar zuwa Aikin Hajjin bana Reviewed by Unknown on August 19, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.