Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya kwashi kwanaki 100 yana jinya a Landan.
Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya
kwashi kwanaki 100 yana jinya a
Landan.
Ofishin shugabancin kasar Najeriya
dake Abuja babban birnin Tarayya ne ya
fitar da wannan sanarwar.
Buhari mai shekaru 74 ya bar kasarsa a
ranar 7 ga watan Yulin shekarar bana,
inda bayan tafiyarsa, fitintinu da dama
suka sake kunno kai a Najeriya tsakanin
yankuna da kuma kabilun kasar.
Mataimakin shugaba Buhari, ya gargadi
jama'a da su daina guntsiri tsoma game
da rashin lafiyar shugaban na Najeriya,
inda ya kara da cewa babu wata cutar
da ke damun sa face ciwon kunne.
A watan Yulin da ya gabata, wasu
kusoshin jam'iyyar Buhari, sun isa
takanas birnin na Landan domin ganin
lafiyar jikinsa, inda suka dawo da
hotuna da kuma fayafan bidiyo, domin
kwantar hankalin al'uma.
Tun a ranar 7 ga watan Agustan
shekarar 2017 ce, a babban birnin
kasar Najeriya Abuja,aka fara gudanar
da zanga-zanga domin Buhari ya
sauka daga kan karagar mulki.
No comments: