Results for General Buhari

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu.

January 05, 2018

A wata wasika da
shugaban Majalisar Dattawan Najeriya,
Bukola Saraki ya karanta a zauren
majalisa, ya sanar da cewa mataimakin
shugaban kasa Yemi Osinbajo, shine zai
gudanar da lamuran ‘kasa a lokacin da
Buhari ya tafi hutu.
Wata takarda da fadar shugaban ‘kasa
ta aikewa manema labarai, na nuna
cewa a lokacin wannan hutu da
shugaba Buhari zai dauka, zai je ganin
likita domin a duba lafiyarsa kamar
yadda aka saba duk shekara.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya
baiwa shugaban kasa damar sanar da
shugaban Majalisar Dattawa da na
Wakilai kafin ya dauki hutu.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Reviewed by Unknown on January 05, 2018 Rating: 5

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya kwashi kwanaki 100 yana jinya a Landan.

August 19, 2017
tw
.Shugaban kasar Najeriya Muhammadu
Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya
kwashi kwanaki 100 yana jinya a
Landan.
Ofishin shugabancin kasar Najeriya
dake Abuja babban birnin Tarayya ne ya
fitar da wannan sanarwar.
Buhari mai shekaru 74 ya bar kasarsa a
ranar 7 ga watan Yulin shekarar bana,
inda bayan tafiyarsa, fitintinu da dama
suka sake kunno kai a Najeriya tsakanin
yankuna da kuma kabilun kasar.
Mataimakin shugaba Buhari, ya gargadi
jama'a da su daina guntsiri tsoma game
da rashin lafiyar shugaban na Najeriya,
inda ya kara da cewa babu wata cutar
da ke damun sa face ciwon kunne.
A watan Yulin da ya gabata, wasu
kusoshin jam'iyyar Buhari, sun isa
takanas birnin na Landan domin ganin
lafiyar jikinsa, inda suka dawo da
hotuna da kuma fayafan bidiyo, domin
kwantar hankalin al'uma.
Tun a ranar 7 ga watan Agustan
shekarar 2017 ce, a babban birnin
kasar Najeriya Abuja,aka fara gudanar
da zanga-zanga domin Buhari ya
sauka daga kan karagar mulki.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya kwashi kwanaki 100 yana jinya a Landan. Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Gida a yau, bayan ya kwashi kwanaki 100 yana jinya a Landan. Reviewed by Unknown on August 19, 2017 Rating: 5

Shugaba Buhari na kan hayar komawa gida yau Assabar

August 19, 2017
center
Fadar shugaban Nigeria ta ce nan gaba a
yau Assabar ne ake sa ran Shugaban kasar
Muhammadu Buhari zai koma kasar bayan
wata doguwar jinya a London.
A cikin wata sanarwa da Mai bai wa
shugaban Shawara kan watsa labarai Femi
Adesina ya fitar ya ce ana sa ran shugaban
ya yi wa 'yan kasar jawabi ta gidajen radiyo
da tallabijin ranar Litinin da safe.
''Ya gode wa daukacin 'yan Nigeria
wadanda suka yi ta yi masa addu'ar samun
lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara
kwantawa ciwo,'' inji takaitacciyar sanarwar
mai sakin layi hudu.
Shugaba Buhari dai ya bar kasar ne ranar 7
ga watan Mayu domin jinyar rashin lafiyar
da ba a bayyana ba; bayan ya mika
ragwamar shugabancin kasar ga
mataimakinsa wanda ya kasance
mukaddashin shugaban kasar tun sannan.
Wannan dai shi ne lokaci mafi tsawo da
wani shugaban kasar ya taba kwashewa
yana jinya a kasar waje kuma dawowar tasa
na zuwa ne 'yan kwanakki bayan da wasu
'yan kasar suka fara zanga-zanga suna kiran
ya dawo ko yayi murabus.
Shugaba Buhari na kan hayar komawa gida yau Assabar Shugaba Buhari na kan hayar komawa gida yau Assabar Reviewed by Unknown on August 19, 2017 Rating: 5
Powered by Blogger.