Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu.


A wata wasika da
shugaban Majalisar Dattawan Najeriya,
Bukola Saraki ya karanta a zauren
majalisa, ya sanar da cewa mataimakin
shugaban kasa Yemi Osinbajo, shine zai
gudanar da lamuran ‘kasa a lokacin da
Buhari ya tafi hutu.
Wata takarda da fadar shugaban ‘kasa
ta aikewa manema labarai, na nuna
cewa a lokacin wannan hutu da
shugaba Buhari zai dauka, zai je ganin
likita domin a duba lafiyarsa kamar
yadda aka saba duk shekara.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya
baiwa shugaban kasa damar sanar da
shugaban Majalisar Dattawa da na
Wakilai kafin ya dauki hutu.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Reviewed by Unknown on January 05, 2018 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.