📚NOVEL📚 AL-MAJIRA 1⃣______To______5⃣


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *DA sunan Allah mai rahma mai jin kai tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi Wa sallam, da Ahlayensa da sahabbansa masu girma* *Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai kowa mai komai da ya bani ikon rubuta wannan dan karamin labari, ina addu'ar Allah ya amfanar da mu abinda yake cikinsa na karuwa, abinda yake na kuskure Allah ya gafarta mana* *wannan labari kirkirarren labari ne an yi shi ne ba don cin mutuncin kowa ba* *gargadi ban yarda a canja min wannan littafi ta kowace irin siga ba, sai da ixnina* *wannan shi ne littafina na farko da na fara rubutawa da fatan xa yi min uxuri idan nayi kuskure*🙏 *Ya Allah kamar yadda na fara wannan rubutu lafiya Allah kasa na gama lpy, Allahu kareni daga sharrin masu sharri*👏🏻👏🏻 *wannan shafin gaba dayanshi sadaukarwa ne gareki yar uwa aminiya kuma Takwara Maijidda bello ana tare🤝💯* 1⃣➖5⃣ *T*afiya take cikin nutsuwa, amma kallo d'aya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin matsananciyar damuwa" yarinya ce 'yar kimanin shekara sha biyar d'auke da buhun bacco a hannunta, tafiya kawai take ba tare da tasan ina ta dosa ba. bakin wata bishiyar darbejiya ta samu ta d'an tsaya domin ta samu hutu ko xuciyarta ta sarara daga tafasar da take yi mata. a hankali ta saukar da ajiyar xuciya sa'annan tayi duba i xuwa jakar da kayanta ke ciki. nan da nan idanuwata suka cika fal da hawaye, ta fad'a a ranta *ALLAH KA FINI SANIN HALIN DA NAKE CIKI* kuka mai tsanani ta cigaba da yi kanta na sunkuye a jikin jakarta, da taga ba sarki sai Allah kukan ba xai kaita ba, sai ta yanke shawarar cigaba da tafiya, duk da dai ba ta ji a ranta xata iya cigaba da tafiyar, saboda yunwa da kishiruwar da suka addabeta. a hankali ta cigaba da jan 'kafa cikin 'karfin hali har ta isa i xuwa wajen da mutane suke, ta samu gefen wajen ta ajiye jakar da 'yan *tsummokaranta* suke ciki. ta 'karasa wajen da wata mai abinci take, da xuwanta sai taga idanun mutane duk sun dawo kanta, cikin hanxari mutanen suka tashi a guje, ciki kuwa har da mai abincin, ashe bisa tsammaninsu suna zaton *MAHAUKACIYA CE* d'aya daga cikinsu ne kawai ya yi 'karfin hali ya'ki guduwa, cikin zafin rai yake tambayarta "ke me kike bukata a nan"??? cikin rawar murya ta amsa masa da cewa "ni *AL-MAJIRAH* ce sadakar abinci ko kudi nake son ku taimaka min dashi tun safe babu abinda nasa a bakina. tsawa ya daka mata wanda yasa har sai da ta firgita "ina ruwanmu da almajirancinki nauyin ciyar da ke a kanmu yake, mu muka sa iyayenki su kawoki bara su wulakanta baiwar da Allah ya basu?? kauce min da gani kafin na doka ball da ke" bata san lokacin da hawaye masu xafi suka rufe idonta ba har ya xamto bata iya ganin hanya, jiri taji ya d'ebeta kamar xata fad'i, Allah dai ya kiyayeta bata fad'i ba. lallai wasu mutanen ba su da tausayi, ta fad'i hakan a ranta. wucewa ta yi kai tsaye wajen da ta ajiye kayanta, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da kuka mai cike da ban tausayi, *KOWANE BAWA DA IRIN YADDA ALLAH YA TSARA MASA RAYUWA* Ni kuma irin tawa jarrabawar kenan ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawa. daukan jakar kayan tayi ta cigaba da tafiya, tana tafiyar tana addu'ar Allah yasa ta samu ko naira goma ne, ta siya abinci su samu abinda xasu kai bakin salati ita da mahaifiyarta, addu'a ta cigaba da yi Allah ya had'ata da wadanda xasu tausaya mata su bata ko da ruwa ne tasha ta ji sanyi a ranta. ranar da ta kara takewa ne yasa ta yanke shawarar tsayawa gudun kada xafin ranar ya cutar da ita, idan rana tayi sanyi ta cigaba daga inda ta tsaya. idan kuma mutane sun gaxa taimaka mata ta siyar da yan tsummokaranta su ci abinci ita da mahaifiyarta bakin wata rumfar mai gyaran takalmi ta samu, tana isowa wajen mai gyaran ya mai da hankali da kallonshi gareta, karasowarta ke da wuya ya mike tsaye ya kasa ko da motsawa, a tuninshi mahaukaciya ce saboda yanayin shigarta da yanayin kayan da suke jikinta ga shi kafarta ko takalmi babu ga kuma jakar tsummokarai a tare da ita . sallamar da tayi masa ita ce ta katse shi daga tunanin da yake yi. har kasa ta tsugunnah "ina yini tace masa" da sauri ya amsa da lafiya" me kike so lafiya?? tace "taimako nake nema yunwa nake ji ka taimaka min dan Allah. har da guntun hawayenta. tunani ya shiga yi. "tabbas wannan yarinyar ba mahaukaciya bace kamar yadda nake tsammani, amma dai duk yadda aka yi yarinyar nan tana cikin matsala, amma ba yadda na iya haka xan kyaleta, watakila iyayenta ne basu shuka alheri ba tunda na ganta a haka, ko kuma guduwa tayi daga gaban iyayenta. amma wane laifi xaka yi wa Allah ya wulakantaka haka, da walakin dai goro a miya (ya manta da cewa Allah shi ne mai tsarawa bawansa rayuwa) maganar da tayi masa "malam nace taimako nake nema" ita ce ta katse masa tunanin da yake yi. ya juyo ya kalleta "nace Allah ya bada hakuri ko ana sadaka dole ne iye"? juyawa tayi da niyyar barin wajen sai taga bai kamata ta cigaba da tafiya a tsananin ranar da ake yi ba, sake tsugunnawa tayi ta roke shi da ya barta ta dan huta idan rana tayi sanyi ta cigaba da tafiya. ranshi bai so ba ya kyaleta ta xauna, saboda a tunaninshi duk wani mai xuwa ya kawo gyara xai tsorata yaki kawowa idan ya ganta. "komawa gefe tayi ta raku6e jikin bango, kamar wadda take shirin tashi a guje, babu abinda zuciyarta ke saqa mata sai yanayin kunci da yanayin da rayuwarta ta shiga ita da mahaifiyarta, idan har rayuwarsu ta cigaba da kasancewa a haka, tasan duk abinda take gudu akwai yiwuwar ya sameta, kiran sallah ne ya katse mata tunanin da take yi, tashi tayi ta nufi wajen mai gyaran nan ta ro'ke shi da ya taimaka mata da ruwan da xa tayi *Alwala* ba musu ya mika mata buta, risinawa tayi cikin ladabi ta karbi butar, ta nufi bakin kwata tahbb tsugunnah ta fara alwalar har ta idar. yadda take jero addu'oin kammala alwala, shi ne ya bawa mai gyaran mamaki, a xuciyarsa ya fada "ikon Allah duk da talauci da damuwar da yarinyar nan take ciki bata fasa neman ilimin sanin lahirarta ba, lallai dole ne na mayar da hankali wajen barin yayana su nemi ilimi saboda halin rayuwa" tana idar da addu'ar ta nufi inda xa tayi sallah ta shimfida dan kwalinta ta hau yin sallah cikin nutsuwa, ta dau lokaci tana yin sallar bayan ta idar tayi addu'a sannan ta shafa............... bayan ta ninke d'an kwalinta sai ta dawo ta zauna ta cigaba da tunanin rayuwa da yadda ta juya musu baya, da mai gyaran takalmin yaga ba tada niyyar tashi ta tafi sai ya kira sunanta "ke *AL-MAJIRAH* karbi naira10 kya sayi abinci tasa hannu biyu ta durkusa har kasa tayi masa godiya mai yawa saboda ko ba komai ta samu kudin da zata siya wa Amminta koda kunu ne. tashi tayi tayi ta cigaba da tafiya tana tafe tana neman taimakon al'umma, masu tausayi sukan taimaka mata, wasu kuma kallonta kawai suke yi ko hakuri basa iya bata a haka har Allah yasa ta sami naira 100 . samun da ta yi ba karamin farin ciki tayi ba, da kudin ta samu ta siya musu abinci ita da Amminta na naira50 kunun 20 sannan ta sayi panadol na naira10 ta juya cikin jindadin samun abincin da ta yi . tana kusanto bakin kangon da suke kwana, yara ta gani cike da bakin kofa, suna jifa da dutse suna tsokanar mahaifiyarta *"mahaukaciya yar macikule"*.......... *mai kwana a bola*.......... *mahaukaciya yar macikule* ...........hawaye ne masu xafi suka kufce mata, bata san lokacin da rufe yaran da duka ba. ganin fusatar da tayi yasa suka fara guduwa, sannan ta kyalesu ta shiga ciki ta rufe kofa. Da sallama ta shiga kangon da suke kwana ita da Amminta hango mahaifiyar tata tayi cikin kaxanta tayi kaca-kaca da wajen da kashin da tayi, har tana kokarin saka kashin a bakinta xa ta ci.. da hanxari ta karasa wajen da take, tana isowa kusa da ita ta bushe da wata irin dariya ta kawo mata duka da hannu, ta jefeta da dutsen da yake kusa da ita. da sauri ta kauce dutsen ya sauka kasa, ta samu ruwa ta wanke mata hannunta da bakinta. shimfida taje tayi mata ta dakkota ta dorata a kan cinyarta ta tallafota tana mata sannu bakinta ta fara kuskure mata sannan ta fara shayar da ita kunun har sai da taga alamar ya isheta, sannan ta hau bata abincin loma biyu kawai tayi ta nuna alamar ya isheta sai ta kyaleta sannan ta goge mata bakinta da wani kyalle. sai *AL-MAJIRAH* ta dauki sauran ta cinye tana ci tana hawaye tana tuna halin da suke ciki ita da Amminta amma nasan babu komai dukkan tsanani yana tare da sauki. *jeeddahtukhaeer*😘😘 ⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳
📚NOVEL📚 AL-MAJIRA 1⃣______To______5⃣ 📚NOVEL📚 AL-MAJIRA  1⃣______To______5⃣ Reviewed by Unknown on January 07, 2018 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.