AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 _*dedication to the intended*_ *Mustapha Mukhtar*😘 *Godiya ta musamman gareki yar uwa rabin jiki Maryam Tijjani Adam* 6⃣➖7⃣ *S*ai ta d'auki naira 20 d'in da ta yi mata saura ta 'kulle a gefen zaninta, tana tuna duk wahalar nan da suke sha na rashin abinci da suttura, ya samo asali ne saboda *kaddarar da Allah ya d'ora musu* da taga yawan damuwar da take yi, yana 'ko'karin ya illata mata xuciyarta da tunaninta, sai ta mayar da komai gefe ta manta da duk wata damuwa, saboda tasan akwai Allah kuma yana sane da bayinsa. "Labari ta shiga bai wa mahaifiyar tata, duk da dai tasan ba fahimta take yi ba, saboda raunin hankalin da take dashi, tana bata labarin sai ta kwashe da dariya kamar tana fahimta, wasu lokutan kuma ta tofa mata miyau ta kai mata duka da 'kafa, a haka tun tana bata labarin har ta gaji tayi shiru. jikinta taji ba 'kwari ta yanke shawarar kwanciya saboda gajiyar da tayi wajen nemo musu abinci, ga shi tana jin alamar ciwon kai saboda ranar da ta wuni tana yawo a cikinta. "A dabarance ta sauke kan mahaifiyarta daga cinyarta ta samu ledar kayanta tayi mata pillow da shi, ita kuma ta qara gyara kwalin da suke xaune ta kwanta. bata fi minti biyar ba bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita, turo 'kofar kangon da aka yi ne ya farkar da ita, yarinya ce matashiya yar kimanin shekara ashirin da biyu ta shigo, hannunta ri'ke da kwano da kuma ba'kar leda. A hankali take sand'ar shigowa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, kasa karasowa tayi ta tsaya daga baya don gudun kada *mahaukaciya*ta biyota. kallon kangon ta shiga yi taga babu komai a ciki sai tarin bola da duwatsu, mamaki ne ya kamata ganin yadda suke kwance cikin 'kazanta ba tare da wata shimfidar kirki ba sai kwali. "yanxu d'an Adam wanda Allah da kansa yace mun karrama shi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, shi ne yake rayuwa a cikin kango kuma kan bola, lallai rayuwa abar tsoro ce" ta fadi haka ne a xuciyarta amma bata sani ba tuni maganar ta fito fili, ganin irin yadda AL-MAJIRA ta tsura mata ido,yasa ta ajiye kwanon abincin da ledar ta fita a guje, a tunaninta tashi xa tayi ta daketa. fitarta ke da wuya ta tashi taje wajen da kayan suke, ta shiga bud'e kwanon abincin, sa taga shinkafa ce da mai da yaji aka kawo musu, ledar kuma kayan sawa ne kala biyu a ciki, da murnarta ta d'auki kwanon ta nufi mahaifiyarta da shi "Ammi kin ga abinda aka kawo mana" ko kallonta bata yi ba, ta cigaba da d'aura leda a 'kafarta tana wasa da yan yatsunta. "Ammi nace kinga an kawo mana abinci da kaya kiyi dariya dan Allah kice kin gode" nan ma dai kallonta ta cigaba da yi kawai, da ta gaji ta mike ta koma ta xauna. A yanxu babu abinda ya fi damunta sama da haukan da Amminta ke yi, ga shi ko magana bata yi ballantana ta samu su rika hira tana bata amsa ko da ta shirme ce, a haka tasan dole xata ri'ka jin saukin damuwarta, kuma xata debe mata kewa. ga shi a yanxu ko maganar tayi mata sai dai duka, da tofa miyau ya biyo baya. "baxan gushe ba ina kulawa da ke har Allah ya karbi rayuwata" ta fadi haka tana shashsheqar kuka". hawaye biyu-biyu ne suka rika bin fusarta tana sharewa, ha'ki'ka a yanxu yadda take ji, babu wani d'an Adam da ya kaita matsala a rayuwar duniya, ta 'kosa Allah ya karbi rayuwarta ta huta da qangin wahalar da suke ciki ita da *Amminta* tasan ba ta kowa ba tada komai, don haka ta gwammace mutuwa watakila idan ta dace sai taji dadi a lahira. kiran sallar magrib ne ya tashe ta tayi alwala, ta tada sallah tana idarwa ta dauki ruwan alwalar taje don ta yi wa Amminta, amma ga mamakinta sai taji tana wani irin gunji alamun bata son ta kusanto da ruwan alwalar gareta. a jiye robar alwalar tayi ta karasa kusa da ita tana xubar da kwallah, Ammina ki tashi nayi miki alwala lokacin sallah ya yi. tureta baya tayi ta fada kan duwatsun da ke wajen, sannan ta cigaba da gunjin nata mai ban tsoro. rushewa da kukan da yarinyar tayi yasa ta tallafota, tana shafa bayanta alamar tana nuna tayi shiru, tausayin mahaifiyarta ne ya kamata, yanxu a ce yadda Ammi take da ibada da son addini yau ita take dukana a kan baxa ta yi sallah ba. kukanta ne ya tsananta ta cigaba da rokon Allah ya bawa mahaifiyarta lafiya, da dukkan masu fama da lalura irin tata. *jeeddahtulkhair*😘
AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣ AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣ Reviewed by Unknown on January 11, 2018 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.