Yana da kyau mata su san yadda ake
hada irin wannan sabulun domin gyaran
jiki ko kuma don sana’a. Yawan shafe –
shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, ya fi
amfani da kuma gyaran fata. A yau mun
kawo muku hanyoyi daban-daban
wadanda za a yi amfani da sabulun salo
don gyaran fata . Abubuwan da za a bukata
â—ŠSabulun salo.
â—ŠZuma
â—ŠBitamin E
â—ŠMan almond. (za a iya samun sa a
shagunan kayan kwalliya) Hadi
A daka sabulun salon ko kuma a saka
abin kankare kubewa a kankare. Sannan
a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun.
Sannan a zuba ‘bitamin E’ da man
‘almond’sai a kwab su sosai. Irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya
ta subul da laushi. Hadi na 2
ΔSabulun salo
ΔMan kadanya
ΔRuwan ganyen ‘aloe bera’
A narka man kadanya a ruwan zafi
sannan a narkar da sabulun salon shi ma. A samu gora a zuba hadin man kadanyar
tare da na man kadanya da ruwan ganyen
‘aloe bera’ sannan a girgiza su domin su
hadu sosai.
Za a iya amfani da shi nan take daga
gama hadi ko kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani da
shi. Hadi na 3
⊙Sabulun salo
⊙Zuma
⊙Kurkum
⊙Man kwakwa
⊙Man Zaitun.
Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan
zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man
kwakwa da kuma man zaitun. A zuba su
a cikin gora sannan a girgiza sosai domin
su hadu sosai,sannan sai a zuba a murta.
Za a iya amfani da wannan hadin nan take ko kuma a jira ya yi tauri bayan sati
biyu sannan a fara amfani da shi.
Wannan hadin yana magance kurajen
gumi ko na fuska da wasu cututtukan
fata.
Allah Yabada Sa'a
No comments: