Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya fara girmama su da nuna musu ladabi da biyayya.
Trump ya yi jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a garin Phoenix inda ya ce, watakila alakar Amurka da Koriya ta Arewa ta dawo daidai.
Babban Kwamandan Sojin Amurka na Tekun Pacific Admiral Harry Harris kuma cewa, ya yi sun zabi hanyar diplomasiyya wajen warware rikicin Nukiliya da makamai masu l,nzami na Koriya ta Arewa.
Kamfanin dillancin labaran na Kyodo kuma ya sanar da cewa, Harris ya yi wa 'yan jarida bayani a sansanin soji na Osan da ke kusa da Seul babban birnin Koriya ta Kudu.
Ya ce, a yanzu sun zabi bin hanyar diplomasiyya don warware rikicinsu da Koriya ta Arewa.
Ya kuma yi nuni da bukatar karfin soji ya taimaka wa aiyukan na diplomasiyya.
Trump: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya fara girmama mu
Reviewed by Unknown
on
August 23, 2017
Rating: 5
Subscribe to:
Post Comments
(
Atom
)
No comments: