Kun san alkhairan da ke cikin kwanaki 10 na watan DZul-Hajji?

Watan DZhul Hijjah shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci, kuma a cikinsa ne ake gudanar da aikin hajji wanda yana cikin shika-shikan musulunci guda biyar da ake so ko wanne musulmi ya yi idan ya samu iko.tw

Daga cikin falalar kwanaki goma na farkon
wannan wata, malamai sun ce an samu
Hadisi daga Manzon Allah SAW da yake
cewa: "Babu wani aiki a wajen ALlah SWT da
yake da matukar lada kamar aikin da bawa
zai yi a kwanakin 10 na farkon Zul Hijja. Sai
Sahabbai suka tambaye shi, 'Ko da kuwa
jihadi ne saboda Allah?' Manzo SAW ya amsa
da cewa, "Ko da kuwa jihadi ne saboda, sai
dai idan mutum ya fita jihadin da dukkan
dukiyarsa ya kuma koma gida ba tare da
komai ba." Bukhari ne ya ruwaito.
Malama da dama sun ce kamar yadda
kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ke
da falala, haka ma kwanaki 10 na farkon Zul
Hijjah ke da falala.
Daga cikin falalarsu kuwa akwai ayyukan da
ake so bawa ya dukufa yi na ibada don
neman yardar Allah.
1. Daga cikin falalar kwanaki 10 na farkon
watan Zul Hijjah akwai yin aikin Hajji'
Aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan
musulunci guda 5, da Allah SWA ya umarci
dukkan musulmai gudanar da shi akalla sau
daya a rayuwarsa.
Aikin Hajji ya wajaba akan wanda ya ke da
lafiyar jiki, da lafiyar yin tafiyar, da kuma
abin da zai yi guzuri da shi, tun daga yin
tafiya zuwa kasa mai tsarki (makka) daga
duk inda ya ke a duniya.
2. Ana so mutum ya yi azumi a kwanaki
taran farko na watan, musamman ma na
ranar Arafah.
Malamai Hussaini Zakariyya ya ce azumin
Arfah yana da falala sosai amma ba farilla ba
ne, amma Ubangiji ya yi alkawarin
gafartawa wanda ya azumci yinin.
3. Ana so a yawaita zikiri da kabbara a
wadannan ranaku 10 na farkon watan Zul
Hijjah.
4. A yawaita yin sallar dare
5. Ana so bawa ya yawaita tuba da neman
gafarar Ubangijinsa.
6. Ana so mutum ya yawaita karatun Al-
qur'ani.
7. Ana so mutum ya kara kaimi wajen yin
kyawawan ayyuka kamar sadaka da taimako
da sauransu.
8. Yin layya a ranar goma ga watan Zul Hijjah
ga wanda yake da halin abin yankawa.
9. Halartar sallar Idi.
10. Yawaita yin godiya ga Allah Subhanahu
wa ta'ala.
Kaza lika akwai batun da ke cewa bai halatta
mutum ya yanke farce ko yin aski ko ga
mace gashinta ya zuba ba idan har akwai
niyyar yin layya.
Sai dai Ustaz Hussain Zakariyya ya ce ba
haka abin yake ba, wancan hukuncin ya hau
kan wadanda suka tafi aikin hajji ne kawai
ban da wadanda ba su samu zuwa ba.
Ga dai Sheikh Hussain Zakariya da karin
bayani, kan abubuwan da ya kamata
musulmi su yi a kwanaki 10 na farkon
watan Hajji, ko da kuwa ba su samu damar
zuwa kasa mai tsarki ba:


tw
Kun san alkhairan da ke cikin kwanaki 10 na watan DZul-Hajji? Kun san alkhairan da ke cikin kwanaki 10 na watan DZul-Hajji? Reviewed by Unknown on August 23, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.