Hanyoyi 31 Da Ma'aurata Zasubi Su Samu Nutsuwa a Gidansu

tw
Assalamu alaikum yan uwana maza da
mata,
(Dam Allah Ku Turawa Yanuwa Suma Su Karu )
(1). mutum ya fara addu'a Allah ya bashi
iyali
na gari, kuma sai shima ya nemi halak
yayi
auren.

(2) bayan tazo ka tambayeta abinda take
so da
wanda bata so
.
(3). sannan kuma duk randa kaci wani abu
a waje baka kawo gida ba idan kazo kace mata naci abu kaza
amma
inaso ki yafe min to zataji dadi a
ranta,sai taje
ashe inada
yanci a gun mijina. .
(4). sannan idan zaka fita matarka tace
mai
gida mai za'a girka,
to ka gaya mata abinda za'a girka,
kakace ta girka ko mai ne
dan wlh sai tayi # danmalele .
(5). sannan ka dunka shawara da matarka
a
kan komai ma

(6). sannan ka damu da halin da zata shiga
misali idan bata da lafiya ka tsaya kayi
jinyarta
duk lokacin da ta juyo ta ganka kusa da
ita
zataji dadi. .
(7). haka itama ta damu da lamarinka idan
bakada lafiya ta tsaya tayi jinyarka kar a
turo
kannen mijin bayan gaki

(8). mace ta zama mai kula da yara,
da kuma tsaftar gida
hakan yanasa mijin hankalinsa ya tashi
idan ba kyanan. .
(9). sannan boye sirrinku yana da
mahimmanci a rayuwar ma'aurata, dan sai kaji wai kawar matar ka tana
cewa
mijin wance bai da karfi,
ko kuma shi mijin ya dunka cewa ai ni
matata ta
iya sex, to wannan yana bata aure.

(10). sannan wadatar zuci, inaso mata ta
zama mai wadatar zuci
duk abinda miji ya kawo wa matarsa to
ta wasa abin
randa kuma babu sai ta hakura
shima ta rarrashe shi
.
(11). tausayin juna lokacin da miji ya
dawo daga gurin aiki ki karbe shi kina masa
sannu ya
gajiya
idan ma da hali rungumi kayanki,
.kaima kuma sai kayi mata sannu da
aikin gida wannan yanasa kaunar ga
ma'aurata.
.
(12). cin abinci tare shima yana daya daga
cikin
abinda yake kawo kauna a gurin ma'arata
.
(13). sai wanka tare da matarka
kuje kuyi wankanku tare yana sa miji
yaji
yana kaunar matarsa itama kuma haka. .

(14). sai iya girki shima babban abu ne
amma sai kaga tace wai bazatai ba zata
nemo "yar aiki
to girkinta zai wasa ko naki.

(15). zama tare da iyalinka kuna hira
shima yana kawo kauna.

(16). kin karbar shawarar abokai da
kawaye, yana kawo nutsuwa a gidan
aure
ku zauna ku magance matsalarku mana.

(17). ragon suna yana kawo matsalar a
rayuwar aure musamman a kasar hausa,
bayan anyi suna kazo ka raba da kanka,
ga
yadda zakai
da farko ka raba naman gida 4 sai ka kira matarka
ta dau kaso daya
sai ka cakuda naman
sai ka sake rabashi gida 5 kuma
sai kace danginka su dau 1
sai na matarka ma 1 sai kaima ka dau 1 sai yaran gida ma 1
sai makota suma 1
shikenan fa ka huta
.
(18). sai wasa da juna yayin mu'amala irin
ta aure, wannan bazanyi bayaninsa sbd ma
bambanta masu karanta rubutun,

(19). raka mata unguwa yana sa taji
mijinta
ya damu da ita kuma ko kofa tazo zata wuce ka bude
mata
zakaga tana taku daya bayan daya

(20). ka dunka girmama nata iyayen
kaima zata girmama naka
sai kuji dadin zaman. .

(21). kazama mai cika alkawari,
idan kace zanzo dashi
to kazo dashi din

(22). mata tazama mai amana kar tayi
aure da niyar
kasuwanci

(23). ka dunka sinbatar matarka #
kisszataji cewa mijinta baya kyamarta

(24). idan kayiwa matarka laifi to ka nuna
kayi
amma tayi hakuri
zataji dadi, karka zama babba da jaka. .

(25). mata ta dunka yiwa mijinta wanki
wannan yanasa miji yaso matarsa.
.
(26). miji ya dunka siyawa matarsa kayan
kwalliya kai harma irinsu rigar nono da fant,
dan waso wlh raban da su siyawa
matansu wannan tun na lefensu da ya
kawo.

(27). kuma miji shima ya zama mai yiwa
matarsa kwanlliya ba sai zai fita ba karka dunka sa jallabiya
.
(28). ku dunka yawan yin wasa a gida
koda
ma na tsere na .
(29). anaso mace ta dunka riga mijinta tashi
daga barci
kuma kafin ya tashi tayi wanka
tayi kwanlliya
to idan ya tashi ya ganta a haka har ya
wuni ita zai dunka gani a ransa
.
(30). miji ya zama mai yiwa matarsa
kyauta
idan tayi masa wani
misali idan tayi ma kwanliya wacce bata saba
yi maka
irinta ba
to sai ka wasa wannan wankan
kuma sai kace ka sai wankan nan muyi
ciniki, to gobe ma zatayi wanda yafi wannan

(31). miji ya zama mai kamin kai
ba ko wacce mace ce zata kulashi ya
kulata
ba,
wannan yanasa mata ta damu da mijinta. Allah Yabada Sa'a
Duk Wanda Yaga Wannan Post Din Ya Taimaka Ya Turawa Yan Uwanshi Suma Su Karu
Hanyoyi 31 Da Ma'aurata Zasubi Su Samu Nutsuwa a Gidansu Hanyoyi 31 Da Ma'aurata Zasubi Su Samu Nutsuwa a Gidansu Reviewed by Unknown on December 16, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.