Tambaya Da Amsa Kyautar Bikin Chirismas: Halal Ko Haram?

tw
Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko
ya halatta su karbi kyautar kiristoci a
ranar kirsimeti,
(dan Allah Ku Turawa Yan Uwan Ku Suma Su Karu)
musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki
a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka
yi dangane da haka:

www.Bornomedia.blogspot.com
1. Baya halatta ga Musulmi ya nuna
farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar
aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantan su.

www.Bornomedia.blogspot.com
2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka
yanka da sunan wannan rana.
www.Bornomedia.blogspot.com

3. Ya halatta ya karbi kautar da za su
bashi a wannan ranar. Kamar yadda ya
halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba
yankawa ake yi ba. Kamar kayan
marmari.

www.Bornomedia.blogspot.com
4. Dalili kuwa shi ne:
A)
Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa
As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa
Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, kautar
idin majusawa Nairuz. Sai ya ce: mene ne
wannan kuma? Sai suka ce masa, ya
Sarkin Muminai yau ranar idin Nairuz ce.
Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin
kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-
Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu
Barzata Al-Aslamy cewa: yana da
makwabta majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da
kyaututtuka gidansa, sai yakan cewa
iyalinsa, yaya abin yake?;
www.Bornomedia.blogspot.com
idan kayan
marmari ne to ku ci, wanda kuma ba
kayan maramari bane, to ku mayar musu
kayansu. C) Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa:
wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce,
muna tare da mata
majusawa masu sana'ar shayar da
jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko
mana
www.Bornomedia.blogspot.com
da kyauta. Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce mata, abin da aka
yanka domin wannan ranar kada ku ci.
Ku ci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna
idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya
hana a karbi kyautarsu. Karbar kyautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk
hukunci daya ne, domin wannan ba shi
ne taimaka musu ba akan aikinsu na
kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil
Mustaqim 2/52.
Sannan a karshe yana da kyau mu fahimci cewa,
www.Bornomedia.blogspot.com
Ba ya halatta musulmi ya
taimaka da yi musu yanka a wannan
ranar. Kuma koda musulmi ne ya yanka
musu ba za a ci ba.
Allah ka shiryar da mu tafarkinka
madaidaici. Kowa ya taimaka wajen yada wannan
sako a matsayin nasa gudunmuwar
www.Bornomedia.blogspot.com
Don't Forget Share this Post To Another Group
Tambaya Da Amsa Kyautar Bikin Chirismas: Halal Ko Haram? Tambaya Da Amsa Kyautar Bikin Chirismas: Halal Ko  Haram? Reviewed by Unknown on December 15, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.