Kalli kayatattun hotunan Adam A. Zango da Maryam Yahaya a gurin bikin Ado Gwanja

October 15, 2018
Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan a gurin liyafar cin abinci ta bikin Ado Gwanja da sahibarshi, Maimunatu, ya nishadantar da jama'ar gurin.
Itama dai jarumar fim din Hausa, Maryam Yahaya da sauran wasu abokan aikin Gwanja sun halarci wajan shagalin, muna fatan Allah yasa ayi a gama lafiya.
Kalli kayatattun hotunan Adam A. Zango da Maryam Yahaya a gurin bikin Ado Gwanja Kalli kayatattun hotunan Adam A. Zango da Maryam Yahaya a gurin bikin Ado Gwanja Reviewed by Unknown on October 15, 2018 Rating: 5

Music Nura M Inuwa : Wasika Da Manya Mata Albums

February 01, 2018

Sababbin Album's na nura m inuwa wato wasika. Da manyan mata Su muka kawo muku to zakuiya daukowa yanxu a kasan nan. Music: Nura M Inuwa Wasika Album Download WASIKA Music: Nura M Inuwa Manyan Mata Album Download MANYAN MATA
Music Nura M Inuwa : Wasika Da Manya Mata Albums Music Nura M Inuwa : Wasika Da Manya Mata Albums Reviewed by Unknown on February 01, 2018 Rating: 5

Video wakar Rarara Mahadi Ya Tsorata Yaki Zuwa Kano: New 2018

January 31, 2018
tw
Image © ArewaMobile.com
Sabuwar wakar/ Video na Rarara Mahadi Ya Tsorata Wannan video ne na wakar Rarara Wanda Yayi Ta Akan Mahadi dan zuwanshi kano Wanda Ba'a Son Ra'ayinshi ba Yaki Zuwa ba hanashi akayi
Batareda Na Cikaku da Tsurutuba Kawai idan Kun saukar kunji batun Kuyi sauraro lafiya
Download MP3 Here
Download 3GP Here

Video wakar Rarara Mahadi Ya Tsorata Yaki Zuwa Kano: New 2018 Video wakar Rarara Mahadi Ya Tsorata Yaki Zuwa Kano: New 2018 Reviewed by Unknown on January 31, 2018 Rating: 5

Music Sabuwar wakar Rarara Mai Taken Mahadi Ya Tsorata

January 31, 2018
tw
Image © daudakahuturarara.com

sabuwar Wakar Shahararren Mawakin Siyasan Nan Mai Suna Rarara Ya Fito da sabuwar Wakarsa Mai Suna. Mahadi ya tsorata Wannan Wakar yayitane Akan tSohon gwamnatin kano wato Kwankwaso Akan Zuwanshi kano da yayi alkawari aka hanashi zuwa shine shima dan adawanshi Rarara yayi wannan Wakarshi izuwa Masoyanshi da Yan adawa Batareda Na Cikaku da Tsurutuba Kawai idan Kun saukar kunji batun Kuyi sauraro lafiya
Music Sabuwar wakar Rarara Mai Taken Mahadi Ya Tsorata Music Sabuwar wakar Rarara Mai Taken Mahadi Ya Tsorata Reviewed by Unknown on January 31, 2018 Rating: 5

AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣

January 11, 2018

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 _*dedication to the intended*_ *Mustapha Mukhtar*😘 *Godiya ta musamman gareki yar uwa rabin jiki Maryam Tijjani Adam* 6⃣➖7⃣ *S*ai ta d'auki naira 20 d'in da ta yi mata saura ta 'kulle a gefen zaninta, tana tuna duk wahalar nan da suke sha na rashin abinci da suttura, ya samo asali ne saboda *kaddarar da Allah ya d'ora musu* da taga yawan damuwar da take yi, yana 'ko'karin ya illata mata xuciyarta da tunaninta, sai ta mayar da komai gefe ta manta da duk wata damuwa, saboda tasan akwai Allah kuma yana sane da bayinsa. "Labari ta shiga bai wa mahaifiyar tata, duk da dai tasan ba fahimta take yi ba, saboda raunin hankalin da take dashi, tana bata labarin sai ta kwashe da dariya kamar tana fahimta, wasu lokutan kuma ta tofa mata miyau ta kai mata duka da 'kafa, a haka tun tana bata labarin har ta gaji tayi shiru. jikinta taji ba 'kwari ta yanke shawarar kwanciya saboda gajiyar da tayi wajen nemo musu abinci, ga shi tana jin alamar ciwon kai saboda ranar da ta wuni tana yawo a cikinta. "A dabarance ta sauke kan mahaifiyarta daga cinyarta ta samu ledar kayanta tayi mata pillow da shi, ita kuma ta qara gyara kwalin da suke xaune ta kwanta. bata fi minti biyar ba bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita, turo 'kofar kangon da aka yi ne ya farkar da ita, yarinya ce matashiya yar kimanin shekara ashirin da biyu ta shigo, hannunta ri'ke da kwano da kuma ba'kar leda. A hankali take sand'ar shigowa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, kasa karasowa tayi ta tsaya daga baya don gudun kada *mahaukaciya*ta biyota. kallon kangon ta shiga yi taga babu komai a ciki sai tarin bola da duwatsu, mamaki ne ya kamata ganin yadda suke kwance cikin 'kazanta ba tare da wata shimfidar kirki ba sai kwali. "yanxu d'an Adam wanda Allah da kansa yace mun karrama shi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, shi ne yake rayuwa a cikin kango kuma kan bola, lallai rayuwa abar tsoro ce" ta fadi haka ne a xuciyarta amma bata sani ba tuni maganar ta fito fili, ganin irin yadda AL-MAJIRA ta tsura mata ido,yasa ta ajiye kwanon abincin da ledar ta fita a guje, a tunaninta tashi xa tayi ta daketa. fitarta ke da wuya ta tashi taje wajen da kayan suke, ta shiga bud'e kwanon abincin, sa taga shinkafa ce da mai da yaji aka kawo musu, ledar kuma kayan sawa ne kala biyu a ciki, da murnarta ta d'auki kwanon ta nufi mahaifiyarta da shi "Ammi kin ga abinda aka kawo mana" ko kallonta bata yi ba, ta cigaba da d'aura leda a 'kafarta tana wasa da yan yatsunta. "Ammi nace kinga an kawo mana abinci da kaya kiyi dariya dan Allah kice kin gode" nan ma dai kallonta ta cigaba da yi kawai, da ta gaji ta mike ta koma ta xauna. A yanxu babu abinda ya fi damunta sama da haukan da Amminta ke yi, ga shi ko magana bata yi ballantana ta samu su rika hira tana bata amsa ko da ta shirme ce, a haka tasan dole xata ri'ka jin saukin damuwarta, kuma xata debe mata kewa. ga shi a yanxu ko maganar tayi mata sai dai duka, da tofa miyau ya biyo baya. "baxan gushe ba ina kulawa da ke har Allah ya karbi rayuwata" ta fadi haka tana shashsheqar kuka". hawaye biyu-biyu ne suka rika bin fusarta tana sharewa, ha'ki'ka a yanxu yadda take ji, babu wani d'an Adam da ya kaita matsala a rayuwar duniya, ta 'kosa Allah ya karbi rayuwarta ta huta da qangin wahalar da suke ciki ita da *Amminta* tasan ba ta kowa ba tada komai, don haka ta gwammace mutuwa watakila idan ta dace sai taji dadi a lahira. kiran sallar magrib ne ya tashe ta tayi alwala, ta tada sallah tana idarwa ta dauki ruwan alwalar taje don ta yi wa Amminta, amma ga mamakinta sai taji tana wani irin gunji alamun bata son ta kusanto da ruwan alwalar gareta. a jiye robar alwalar tayi ta karasa kusa da ita tana xubar da kwallah, Ammina ki tashi nayi miki alwala lokacin sallah ya yi. tureta baya tayi ta fada kan duwatsun da ke wajen, sannan ta cigaba da gunjin nata mai ban tsoro. rushewa da kukan da yarinyar tayi yasa ta tallafota, tana shafa bayanta alamar tana nuna tayi shiru, tausayin mahaifiyarta ne ya kamata, yanxu a ce yadda Ammi take da ibada da son addini yau ita take dukana a kan baxa ta yi sallah ba. kukanta ne ya tsananta ta cigaba da rokon Allah ya bawa mahaifiyarta lafiya, da dukkan masu fama da lalura irin tata. *jeeddahtulkhair*😘
AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣ AL-MAJIRA 6⃣↔7⃣ Reviewed by Unknown on January 11, 2018 Rating: 5

📚NOVEL📚 AL-MAJIRA 1⃣______To______5⃣

January 07, 2018

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *DA sunan Allah mai rahma mai jin kai tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi Wa sallam, da Ahlayensa da sahabbansa masu girma* *Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai kowa mai komai da ya bani ikon rubuta wannan dan karamin labari, ina addu'ar Allah ya amfanar da mu abinda yake cikinsa na karuwa, abinda yake na kuskure Allah ya gafarta mana* *wannan labari kirkirarren labari ne an yi shi ne ba don cin mutuncin kowa ba* *gargadi ban yarda a canja min wannan littafi ta kowace irin siga ba, sai da ixnina* *wannan shi ne littafina na farko da na fara rubutawa da fatan xa yi min uxuri idan nayi kuskure*🙏 *Ya Allah kamar yadda na fara wannan rubutu lafiya Allah kasa na gama lpy, Allahu kareni daga sharrin masu sharri*👏🏻👏🏻 *wannan shafin gaba dayanshi sadaukarwa ne gareki yar uwa aminiya kuma Takwara Maijidda bello ana tare🤝💯* 1⃣➖5⃣ *T*afiya take cikin nutsuwa, amma kallo d'aya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin matsananciyar damuwa" yarinya ce 'yar kimanin shekara sha biyar d'auke da buhun bacco a hannunta, tafiya kawai take ba tare da tasan ina ta dosa ba. bakin wata bishiyar darbejiya ta samu ta d'an tsaya domin ta samu hutu ko xuciyarta ta sarara daga tafasar da take yi mata. a hankali ta saukar da ajiyar xuciya sa'annan tayi duba i xuwa jakar da kayanta ke ciki. nan da nan idanuwata suka cika fal da hawaye, ta fad'a a ranta *ALLAH KA FINI SANIN HALIN DA NAKE CIKI* kuka mai tsanani ta cigaba da yi kanta na sunkuye a jikin jakarta, da taga ba sarki sai Allah kukan ba xai kaita ba, sai ta yanke shawarar cigaba da tafiya, duk da dai ba ta ji a ranta xata iya cigaba da tafiyar, saboda yunwa da kishiruwar da suka addabeta. a hankali ta cigaba da jan 'kafa cikin 'karfin hali har ta isa i xuwa wajen da mutane suke, ta samu gefen wajen ta ajiye jakar da 'yan *tsummokaranta* suke ciki. ta 'karasa wajen da wata mai abinci take, da xuwanta sai taga idanun mutane duk sun dawo kanta, cikin hanxari mutanen suka tashi a guje, ciki kuwa har da mai abincin, ashe bisa tsammaninsu suna zaton *MAHAUKACIYA CE* d'aya daga cikinsu ne kawai ya yi 'karfin hali ya'ki guduwa, cikin zafin rai yake tambayarta "ke me kike bukata a nan"??? cikin rawar murya ta amsa masa da cewa "ni *AL-MAJIRAH* ce sadakar abinci ko kudi nake son ku taimaka min dashi tun safe babu abinda nasa a bakina. tsawa ya daka mata wanda yasa har sai da ta firgita "ina ruwanmu da almajirancinki nauyin ciyar da ke a kanmu yake, mu muka sa iyayenki su kawoki bara su wulakanta baiwar da Allah ya basu?? kauce min da gani kafin na doka ball da ke" bata san lokacin da hawaye masu xafi suka rufe idonta ba har ya xamto bata iya ganin hanya, jiri taji ya d'ebeta kamar xata fad'i, Allah dai ya kiyayeta bata fad'i ba. lallai wasu mutanen ba su da tausayi, ta fad'i hakan a ranta. wucewa ta yi kai tsaye wajen da ta ajiye kayanta, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da kuka mai cike da ban tausayi, *KOWANE BAWA DA IRIN YADDA ALLAH YA TSARA MASA RAYUWA* Ni kuma irin tawa jarrabawar kenan ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawa. daukan jakar kayan tayi ta cigaba da tafiya, tana tafiyar tana addu'ar Allah yasa ta samu ko naira goma ne, ta siya abinci su samu abinda xasu kai bakin salati ita da mahaifiyarta, addu'a ta cigaba da yi Allah ya had'ata da wadanda xasu tausaya mata su bata ko da ruwa ne tasha ta ji sanyi a ranta. ranar da ta kara takewa ne yasa ta yanke shawarar tsayawa gudun kada xafin ranar ya cutar da ita, idan rana tayi sanyi ta cigaba daga inda ta tsaya. idan kuma mutane sun gaxa taimaka mata ta siyar da yan tsummokaranta su ci abinci ita da mahaifiyarta bakin wata rumfar mai gyaran takalmi ta samu, tana isowa wajen mai gyaran ya mai da hankali da kallonshi gareta, karasowarta ke da wuya ya mike tsaye ya kasa ko da motsawa, a tuninshi mahaukaciya ce saboda yanayin shigarta da yanayin kayan da suke jikinta ga shi kafarta ko takalmi babu ga kuma jakar tsummokarai a tare da ita . sallamar da tayi masa ita ce ta katse shi daga tunanin da yake yi. har kasa ta tsugunnah "ina yini tace masa" da sauri ya amsa da lafiya" me kike so lafiya?? tace "taimako nake nema yunwa nake ji ka taimaka min dan Allah. har da guntun hawayenta. tunani ya shiga yi. "tabbas wannan yarinyar ba mahaukaciya bace kamar yadda nake tsammani, amma dai duk yadda aka yi yarinyar nan tana cikin matsala, amma ba yadda na iya haka xan kyaleta, watakila iyayenta ne basu shuka alheri ba tunda na ganta a haka, ko kuma guduwa tayi daga gaban iyayenta. amma wane laifi xaka yi wa Allah ya wulakantaka haka, da walakin dai goro a miya (ya manta da cewa Allah shi ne mai tsarawa bawansa rayuwa) maganar da tayi masa "malam nace taimako nake nema" ita ce ta katse masa tunanin da yake yi. ya juyo ya kalleta "nace Allah ya bada hakuri ko ana sadaka dole ne iye"? juyawa tayi da niyyar barin wajen sai taga bai kamata ta cigaba da tafiya a tsananin ranar da ake yi ba, sake tsugunnawa tayi ta roke shi da ya barta ta dan huta idan rana tayi sanyi ta cigaba da tafiya. ranshi bai so ba ya kyaleta ta xauna, saboda a tunaninshi duk wani mai xuwa ya kawo gyara xai tsorata yaki kawowa idan ya ganta. "komawa gefe tayi ta raku6e jikin bango, kamar wadda take shirin tashi a guje, babu abinda zuciyarta ke saqa mata sai yanayin kunci da yanayin da rayuwarta ta shiga ita da mahaifiyarta, idan har rayuwarsu ta cigaba da kasancewa a haka, tasan duk abinda take gudu akwai yiwuwar ya sameta, kiran sallah ne ya katse mata tunanin da take yi, tashi tayi ta nufi wajen mai gyaran nan ta ro'ke shi da ya taimaka mata da ruwan da xa tayi *Alwala* ba musu ya mika mata buta, risinawa tayi cikin ladabi ta karbi butar, ta nufi bakin kwata tahbb tsugunnah ta fara alwalar har ta idar. yadda take jero addu'oin kammala alwala, shi ne ya bawa mai gyaran mamaki, a xuciyarsa ya fada "ikon Allah duk da talauci da damuwar da yarinyar nan take ciki bata fasa neman ilimin sanin lahirarta ba, lallai dole ne na mayar da hankali wajen barin yayana su nemi ilimi saboda halin rayuwa" tana idar da addu'ar ta nufi inda xa tayi sallah ta shimfida dan kwalinta ta hau yin sallah cikin nutsuwa, ta dau lokaci tana yin sallar bayan ta idar tayi addu'a sannan ta shafa............... bayan ta ninke d'an kwalinta sai ta dawo ta zauna ta cigaba da tunanin rayuwa da yadda ta juya musu baya, da mai gyaran takalmin yaga ba tada niyyar tashi ta tafi sai ya kira sunanta "ke *AL-MAJIRAH* karbi naira10 kya sayi abinci tasa hannu biyu ta durkusa har kasa tayi masa godiya mai yawa saboda ko ba komai ta samu kudin da zata siya wa Amminta koda kunu ne. tashi tayi tayi ta cigaba da tafiya tana tafe tana neman taimakon al'umma, masu tausayi sukan taimaka mata, wasu kuma kallonta kawai suke yi ko hakuri basa iya bata a haka har Allah yasa ta sami naira 100 . samun da ta yi ba karamin farin ciki tayi ba, da kudin ta samu ta siya musu abinci ita da Amminta na naira50 kunun 20 sannan ta sayi panadol na naira10 ta juya cikin jindadin samun abincin da ta yi . tana kusanto bakin kangon da suke kwana, yara ta gani cike da bakin kofa, suna jifa da dutse suna tsokanar mahaifiyarta *"mahaukaciya yar macikule"*.......... *mai kwana a bola*.......... *mahaukaciya yar macikule* ...........hawaye ne masu xafi suka kufce mata, bata san lokacin da rufe yaran da duka ba. ganin fusatar da tayi yasa suka fara guduwa, sannan ta kyalesu ta shiga ciki ta rufe kofa. Da sallama ta shiga kangon da suke kwana ita da Amminta hango mahaifiyar tata tayi cikin kaxanta tayi kaca-kaca da wajen da kashin da tayi, har tana kokarin saka kashin a bakinta xa ta ci.. da hanxari ta karasa wajen da take, tana isowa kusa da ita ta bushe da wata irin dariya ta kawo mata duka da hannu, ta jefeta da dutsen da yake kusa da ita. da sauri ta kauce dutsen ya sauka kasa, ta samu ruwa ta wanke mata hannunta da bakinta. shimfida taje tayi mata ta dakkota ta dorata a kan cinyarta ta tallafota tana mata sannu bakinta ta fara kuskure mata sannan ta fara shayar da ita kunun har sai da taga alamar ya isheta, sannan ta hau bata abincin loma biyu kawai tayi ta nuna alamar ya isheta sai ta kyaleta sannan ta goge mata bakinta da wani kyalle. sai *AL-MAJIRAH* ta dauki sauran ta cinye tana ci tana hawaye tana tuna halin da suke ciki ita da Amminta amma nasan babu komai dukkan tsanani yana tare da sauki. *jeeddahtukhaeer*😘😘 ⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳⏳
📚NOVEL📚 AL-MAJIRA 1⃣______To______5⃣ 📚NOVEL📚 AL-MAJIRA  1⃣______To______5⃣ Reviewed by Unknown on January 07, 2018 Rating: 5

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu.

January 05, 2018

A wata wasika da
shugaban Majalisar Dattawan Najeriya,
Bukola Saraki ya karanta a zauren
majalisa, ya sanar da cewa mataimakin
shugaban kasa Yemi Osinbajo, shine zai
gudanar da lamuran ‘kasa a lokacin da
Buhari ya tafi hutu.
Wata takarda da fadar shugaban ‘kasa
ta aikewa manema labarai, na nuna
cewa a lokacin wannan hutu da
shugaba Buhari zai dauka, zai je ganin
likita domin a duba lafiyarsa kamar
yadda aka saba duk shekara.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya
baiwa shugaban kasa damar sanar da
shugaban Majalisar Dattawa da na
Wakilai kafin ya dauki hutu.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai tafi hutu har na tsawon kwanaki goma daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairu. Reviewed by Unknown on January 05, 2018 Rating: 5

Yadda Ake Amfani Da Sabulun Salo Don Gyaran Fata.

December 22, 2017
tw
Yana da kyau mata su san yadda ake
hada irin wannan sabulun domin gyaran
jiki ko kuma don sana’a. Yawan shafe –
shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, ya fi
amfani da kuma gyaran fata. A yau mun
kawo muku hanyoyi daban-daban
wadanda za a yi amfani da sabulun salo
don gyaran fata . Abubuwan da za a bukata

◊Sabulun salo.
◊Zuma
◊Bitamin E
◊Man almond.
(za a iya samun sa a
shagunan kayan kwalliya) Hadi
A daka sabulun salon ko kuma a saka
abin kankare kubewa a kankare. Sannan
a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun.
Sannan a zuba ‘bitamin E’ da man
‘almond’sai a kwab su sosai. Irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya
ta subul da laushi. Hadi na 2


ΔSabulun salo

ΔMan kadanya

ΔRuwan ganyen ‘aloe bera’
A narka man kadanya a ruwan zafi
sannan a narkar da sabulun salon shi ma. A samu gora a zuba hadin man kadanyar
tare da na man kadanya da ruwan ganyen
‘aloe bera’ sannan a girgiza su domin su
hadu sosai.
Za a iya amfani da shi nan take daga
gama hadi ko kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani da
shi. Hadi na 3


⊙Sabulun salo

⊙Zuma

⊙Kurkum

⊙Man kwakwa

⊙Man Zaitun.
Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan
zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man
kwakwa da kuma man zaitun. A zuba su
a cikin gora sannan a girgiza sosai domin
su hadu sosai,sannan sai a zuba a murta.
Za a iya amfani da wannan hadin nan take ko kuma a jira ya yi tauri bayan sati
biyu sannan a fara amfani da shi.
Wannan hadin yana magance kurajen
gumi ko na fuska da wasu cututtukan
fata.
Allah Yabada Sa'a
Yadda Ake Amfani Da Sabulun Salo Don Gyaran Fata. Yadda Ake Amfani Da Sabulun Salo Don  Gyaran Fata. Reviewed by Unknown on December 22, 2017 Rating: 5
Powered by Blogger.